Gwamna Tambuwal ya zabi sabon mataimakinsa

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Tambuwal ya zabi sabon mataimakinsa Alhaji Manir Dan’iya don maye gurbin tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Alhaji Ahmed Aliyu, wanda ya yi murabus ranar 13 ga watan Nuwamba 2018. Majiyar Kamfanin Dillancin Labarai NAN ta bayyana cewa, Gwamna Tambuwal ya mika wa kakakin majalisar dokokin jihar Alhaji Salihu Maidaji takardar amincewa da […]

Gwamna Tambuwal ya zabi sabon mataimakinsa

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Tambuwal ya zabi sabon mataimakinsa Alhaji Manir Dan’iya don maye gurbin tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Alhaji Ahmed Aliyu, wanda ya yi murabus ranar 13 ga watan Nuwamba 2018.

Majiyar Kamfanin Dillancin Labarai NAN ta bayyana cewa, Gwamna Tambuwal ya mika wa kakakin majalisar dokokin jihar Alhaji Salihu Maidaji takardar amincewa da sabon Mataimakin.