Gwamna Wamakko ya shawarci shugabannin sojoji su ajiye mukamansu

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko ya shawarci shugabannin tsaron Najeriya su a jiye mukamansu ciki har da shugaban ’yan sandan kasar saboda gazawarsu da ta sanya aka dage zaben kasar da aka shata gudanarwa a gobe.Gwamna Wamakko ya ce dukansu ya kamata su ajiye mukamansu don sun kassara kasar nan ta hanyar gaza […]

Gwamna Wamakko ya shawarci shugabannin sojoji su ajiye mukamansu
Gwamna Wamakko ya shawarci shugabannin sojoji su ajiye mukamansu

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko ya shawarci shugabannin tsaron Najeriya su a jiye mukamansu ciki har da shugaban ’yan sandan kasar saboda gazawarsu da ta sanya aka dage zaben kasar da aka shata gudanarwa a gobe.
Gwamna Wamakko ya ce dukansu ya kamata su ajiye mukamansu don sun kassara kasar nan ta hanyar gaza sauke nauyin da aka aza musu “Ku yi ajewar mutunci shi ne zai fiye muku don kun gaza gudanar da aikinku,” inji shi.
Gwamna Wamakko ya zargi Jam’iyyar PDP da hannu a dage zaben don ta tabbatar in aka gudanar da zaben a lokacin da aka sanya da farko, to lallai za ta fadi, ya ce ta manta dagewar ba za ta hana a kayar da su ba.
“Laya ba ta maganin mutuwa, don haka mutanen kasar nan ba su yi mamakin haka ba, yadda za a ce matsalar tsaro da aka share shekaru ana fama da ita wai za a magance ta cikin mako shida.”
Ya ba ’yan jam’iyyarsu hakuri inda ya ce su zama masu bin doka da oda, kuma ya roki Allah Ya isar wa jama’ar Jihar Sakkwato kan zaluncin da Mai ba Shugaban kasa Shawara kan Harkar Tsaro ke yi na bata sunan jihar a a idon jama’ar kasar nan.