Gwamna ya bayar da wa’adi ga mahauta su koma sabuwar mayanka
Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo ya bayar da wa’adin zuwa karshen wannan wata na Afrilu ga dukkan mahautan da ke sana’ar fawa a kananan hukumomi 11 na masarautar Ibadan da su koma sabuwar mayankar zamani da gwamnati ta kashe miliyoyin Naira wajen ginawa a kauyen Akinyele domin tsaftace naman dabbobi da ake yankawa a […]

Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo ya bayar da wa’adin zuwa karshen wannan wata na Afrilu ga dukkan mahautan da ke sana’ar fawa a kananan hukumomi 11 na masarautar Ibadan da su koma sabuwar mayankar zamani da gwamnati ta kashe miliyoyin Naira wajen ginawa a kauyen Akinyele domin tsaftace naman dabbobi da ake yankawa a kulluyaumin a birnin Ibadan.
Gwamnan ya bayar da wa’adin ne cikin jawabin da ya yi wa taron masu ruwa da tsaki a kan matsalar yankan dabbobi a wurare masu kazanta. Ya ce, sabuwar mayankar ta zamani ce da ta samar da kwararrun jami’ai masu kula da lafiyar dabbobi da wuraren yanka da fidar dabbobi masu tsafta da samar da ayyuka ga matasa tare da samar da kudin shiiga aljihun gwamnati da kawo karshen rikici a tsakanin makiyaya da manoma.
Gwamnati ta kira wannan taro ne domin tattaunawa a kan lalubo hanya mafi sauki wajen komawa sabuwar mayankar da ake son dukkan masu sana’ar fawa a cikin kananan hukumomi 11 na masarautar Ibadan su goyi bayan gwamnati ba kamar yadda makiya ci gaban wannan yanki suke baza jita-jita mara kan gado ba, inji shi.
Ya ce, sabuwar mayankar ta hadin guiwa ce a tsakanin wani kamfani mai zaman kansa mai suna C & E Consulting Ltd mai kashi 50 da gwamnatin jihar mai kashi 10 da kananan hukumomi 11 da hukumomin raya alkarya LCDA suke da kashi 36 da kungiyar mahauta mai kashi 4 na mallakar sabuwar mayankar.
“Ina tabbatar maku cewa, samar da sabuwar mayankar alama ce ta kawo karshen rikici tsakanin manoma da makiyaya a Jihar Oyo domin daga yanzu za a rika yin jigilar shanu da sauran dabbobi kai tsaye ne zuwa wannan mayanka a maimakon ratsawa cikin kauyuka da garuruwa da dabbobin suke lalata amfanin gonaki a baya,” inji Gwamnan.
“Haka kuma ina farin cikin ganin samar da sabuwar mayankar zai canza salon tallar nama mai dauke da cututtuka a cikin kasuwanni da unguwanni,” inji shi.
Ya ce daga yanzu mahauta za su fara biyan Naira dubu 3 da dari 5 ga kowace saniya da aka yanka a cikin sabuwar mayankar ta Akinyele.
Jagoran mahauta a sashen Kudu maso Yammacin kasa Alhaji Biliaminu Elesinmeta ya nemi gwamnan ya taimaka wajen rage sabon harajin yankar saniya guda 1 da ya ambata.