Gwamna ya kama sojoji da ‘yan sanda na karbar na goro
Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum, ya kama wasu sojoji da ‘yan sanda na karbar na goro a hannun fasinjoji bayan tare matafiya da dama a hanyar. A cewar fasinjojin jami’an tsaron na karbar Naira dubu daya ne a hannun su, idan mutum bai da katin shaida. Gwamnan ya kama jami’an tsaron ne lokacin da yake […]
Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum, ya kama wasu sojoji da ‘yan sanda na karbar na goro a hannun fasinjoji bayan tare matafiya da dama a hanyar.
A cewar fasinjojin jami’an tsaron na karbar Naira dubu daya ne a hannun su, idan mutum bai da katin shaida.
Gwamnan ya kama jami’an tsaron ne lokacin da yake hanyarsa ta zuwa kauyen Jakana wanda yake da nisan kilomita 45 zuwa Maiduguri babban birnin jihar don ziyartar kauyen bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari ranar Asabar da ta gabata.