Gwamna ya kare nada ’ya’yan sarakuna bisa mukaman kwamishinoni a jiharsa
Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo ya kare nada ’ya’yan manyan sarakuna bisa mukaman kwamishinoni da cewa sun cancanta ne, kuma babu daya daga cikin iyayensu da ya nemi alfarmar hakan.Gwamnan ya fadi haka ne cikin jawabinsa ga tawagar wasu sarakuna a karkashin jagorancin Alaafin na Oyo da suka kai masa gaisuwar ban girma a […]

Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo ya kare nada ’ya’yan manyan sarakuna bisa mukaman kwamishinoni da cewa sun cancanta ne, kuma babu daya daga cikin iyayensu da ya nemi alfarmar hakan.
Gwamnan ya fadi haka ne cikin jawabinsa ga tawagar wasu sarakuna a karkashin jagorancin Alaafin na Oyo da suka kai masa gaisuwar ban girma a ofishinsa a Ibadan a karshen mako. “Ina sane da maganganu da wasu mutane ke yi dangane da nada ’ya’yan sarakuna bisa mukaman kwamishinoni da na yi. Ina tabbatar da cewa, ni da kaina na nada su, babu daya daga cikin iyayensu da ya tuntube ni domin neman alfarma. Na yi haka ne saboda ganin kyawawan halaye da gogewar ayyukan da suka yi a baya, na tabbatar da cancantarsu kuma muke matukar alfahari da su. Kuma, wannan nadi wata hanya ce ta kara girmamawa ga sarakuna da goyon bayan al’adunmu tare da irin gudunmawar da zuriyar masarautun suke bayarwa ga ci gaban Jihar Oyo.”
Gwamnan ya nuna farin cikinsa ga Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Alayiwola Adeyemi, wanda ya jagoranci wasu sarakuna domin kai masa gaisuwar ban girma, lamarin da ya ce zai karfafa masa guiwar ci gaba da gudanar da ayyukan ci gaban al’ummar jihar.
Tun farko a cikin jawabinsa, Alaafin din ya danganta ziyarar tasu kan jinjina wa namijin kokarin da gwamnan yake yi na gudanar da ayyukan ci gaba a jihar. Dangane da nadin kwamishinonin, sarkin ya ce salo ne irin wanda Cif Obafemi Awolowo ya aiwatar a gwamnatinsa a jumhuriya ta farko.