Gwamna ya yafe wa malaman makaranta 1,000, sun koma aiki

Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo ya yafe wa malaman makarantun sakandare su fiye da dubu daya da hukumar lura da malamai (TESCOM) ta kora daga aiki kwanan baya a dalilin shekarun bogi da suka rubuta a cikin takardun neman aiki. Gwamnan ya bayar da umarnin dawo da malaman a kan aikinsu ne a ranar […]

Gwamna ya yafe wa malaman makaranta 1,000, sun koma aiki

Wani sashe na korarrun malaman makarantun sakandare da aka yi wa ahuwaGwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo ya yafe wa malaman makarantun sakandare su fiye da dubu daya da hukumar lura da malamai (TESCOM) ta kora daga aiki kwanan baya a dalilin shekarun bogi da suka rubuta a cikin takardun neman aiki. Gwamnan ya bayar da umarnin dawo da malaman a kan aikinsu ne a ranar Talata a lokacin da yake yi musu bayanin matsayin gwamnati a kan wannan muhimmiyar matsala.
Gwamnan, wanda ya tausaya wa  halin da korarrun malaman suka fada tun daga lokacin da aka kore su, ya ce gwamnatinsa ta kafa kwamitin da zai binciki gaskiyar shekarun malaman, don yin gyare-gyare na mayar da wasu bakin aikinsu, sannan a yi wa wasu ritaya. Ya ce, fafutukar kungiyar malaman makarantu (NUT) ta jihar da tsoma bakin wasu dattijai yana daga abubuwan da gwamnati ta duba ta dauki matakin yafiya ga malaman, saboda gwamnatinsa na daukar ilmi da muhimmanci.
daruruwan malaman sun yi ta rera wakokin nuna murna da godiya da wannan mataki da Gwamna Ajimobi, har wadansunsu suka rika kukan dadi.
Da yake nuna godiya cikin wata takardar sanarwa da sakataren kungiyar malamai, Kwamared Waheed Olojede ya sanya wa hannu, ya jinjina wa matakin tausayawa da sauraron koke-koken kungiyar tun farko da gwamnan ya yi. Ya ce, irin wannan mataki ake bukatar shugabanni su rika dauka wajen sauraron halin da talakawansu ke ciki tare da share musu hawaye.