Gwamna ya yi takaddama da tsohon Gwamna kan mayar wa Hukumar EFCC Naira miliyan 500

A Litinin da ta wuce ne jaridar The Nation ta buga wani labari da tayi hira da Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, inda ya ce tsohon Gwamnan Jihar Sanata Rasheed Ladoja, ya mayar da kudi Naira miliyan dari 500 mallakar gwamnatin jihar ga Hukumar Yaki da yi wa tattlain arziki ta’annati, ta EFCC. Kwana […]

Gwamna ya yi takaddama da tsohon Gwamna kan mayar wa Hukumar EFCC Naira miliyan 500
Gwamna ya yi takaddama da tsohon Gwamna kan mayar wa Hukumar EFCC Naira miliyan 500

A Litinin da ta wuce ne jaridar The Nation ta buga wani labari da tayi hira da Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, inda ya ce tsohon Gwamnan Jihar Sanata Rasheed Ladoja, ya mayar da kudi Naira miliyan dari 500 mallakar gwamnatin jihar ga Hukumar Yaki da yi wa tattlain arziki ta’annati, ta EFCC. Kwana daya tsakani sai Sanata Rasheed Ladoja, ya karyata wannan zance da yake cewa, sharri aka yi mishi domin a bata mishi suna saboda shi dai ya sani cewa, bai taba mayar da wasu kudi ga EFCC, asl’amarin dai ya haifar da takaddama.

Ya ce, idan akwai kamshin gaskiya to, a fito da shaidar da za ta tabbatar da hakan, Ilai kuwa a ranar Talata sai Gwamna Abiola Ajimobi ta hannun Sakataren Gwamnati, Mista Ishmael Olalekan Alli, ya fito da wasu cakin kudi da aka biya a wasu bankuna da suke tabbatar da mayar da wadannan kudi ga Hukumar ta EFCC da tsohon Gwamnan yayi a Litinin din da ta wuce ne.
A binciken da Wakilinmu ya gudanar a cikin kwanaki uku da fara wannan tonon silili, ya gano cewa, yanzu haka fitattun ‘yan siyasa hudu, wato, Gwamna da ke kan gado Sanata Abiola Ajimobi na APC da tsohon Gwamna Sanata Rasheed Ladoja na jam’iyyar Accord da Sanata Teslim Folarin na PDP da Injiniya Seyi Makinde na SDP, dukkansu ‘yan asalin birnin Ibadan ne, inda kowane ya samu tikitin tsayawa takarar Gwamna a zabe mai zuwa, wanda hakan ya haifar da bi ta da kulli da suke yi wa juna da zafafan kalamai. A waje daya kuma tsohon Gwamna Christopher Alao Akala, dan asalin Ogbomoso, wanda ya sha kaye a zaben fitar da gwani na PDP ya fusata ya kaurace zuwa jam’iyyar Labour, wacce ta ba shi irin wannan tikitin fafatawa a tsakaninsa da mutanen hudu ‘yan Ibadan da ke neman wannan kujera ta Gwamna a zaben watan gobe.
Wani dan siyasa mai suna Solomon Adeleke, ya ce, “salon da ‘yan siyasa suka dauka a Najeriya na bata sunan junansu abin kunya ne da ba zai kaimu ga nasarar samun dimokuradiyya da muke fatan samu a nan gaba ba.
“Ni ban ga dalilin shafa kashin kaji da suke yi wa junansu ba. Wannan yana nuna rashin gaskiyarsu a fili da rashin kishin kasar haihuwarsu. Kamata yayi kowace jam’iya da ‘yan takarar mukamanta su fito su bayyanawa magoya bayansu gaskiya na irin muhimman abubuwan da za su iya samar wa idan sun yi nasara. Ya kamata su gane cewa, yanzu fa kan mage ya waye domin jama’ar kasar nan sun gaji da irin wadannan bakaken maganganu,” inji shi.
Ita kuwa Bashirat Alalade, karamar ‘yar kasuwa, ta soki lamirin irin wannan dabi’a ta ’yan siyasar.
“Akwai mata kawayena ne da muka kafa wata kungiya a boye, muna bin kowane lungu, muna wayar da kan mutane masu kishin kasa da su zabi mutane na kwarai masu son ci gabansu, amma ba baragurbi da za su mayar da hannun agogo baya ba. Bai kamata shugabanni su rika fitowa suna bata sunayen juna ba. Ku fito ku nuna mana gaskiyar irin abubuwan taimako da ci gaban jama’a da kuka yi a cikin gidanku da unguwanni da kauyuka da birane. Idan kuka yi hakan ne za mu duba mu ga wanda yafi cancanta mu zaba a kan kowane mukami amma ba zage zagen juna da kuke koyawa matasa miyagun abubuwan da ba zai amfani rayuwarsu a nan gaba ba. Kuma babu ruwanmu da bangaranci domin cancanta kawai muka sanya a gaba a wannan aiki da kume yi ta karkashin kasa,” inji ta.