Gwamna ya yi wa iyalan ’yan wasan Kano da suka rasu a hatsari goma ta arziki
’Yan wasan sun yi hatsari ne a yayin da suke dawowa daga gasar wasannin ƙasa ta National Sports Festival da aka gudanar a Jihar Ogun.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da kyautar fuloti da kuɗi naira miliyan biyar ga kowane ɗaya daga cikin iyalan tawagar ’yan wasan nan na Kano 22 da suka rasu a wani mummunan haɗarin mota da ya auku a watan Yuni.
Mai bai wa gwamnan shawara kan yaɗa labarai, Ibrahim Adam, ne ya tabbatar da wannan kyauta cikin wani saƙo da ya wallafa a Facebook a wannan Larabar.
- Ministocin Ghana biyu sun rasu a hatsarin jirgin sama
- Gwamnan Kano ya gargaɗi muƙarrabansa bayan murabus ɗin Kwamishina
“Mai girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bai wa iyalan ’yan wasan da suka rasu fuloti ɗaya da kuma naira miliyan biyar kowannensu,” in ji sanarwar.
Aminiya ta ruwaito cewa, tawagar ’yan wasan da suka rasu ta yi hatsari ne a yayin da suke dawowa daga gasar wasannin ƙasa ta National Sports Festival da aka gudanar a Jihar Ogun.
Tawagar da lamarin ya rutsa da ita ta ƙunshi ’yan wasa, masu horarwa, mataimakansu, jami’an lafiya, direbobi, injiniyoyi da kuma ɗan jarida.
Ajali ya katse musu hanzari ne bayan samun nasarori daban-daban a gasar ta National Sports Festival da suka haɗa da sarƙoƙin zinare 6, azurfa 13 da na tagulla 10 da suka lashe.
Ana iya tuna cewa, mummunan lamarin ya auku ne a garin Dakatsalle da ke ƙaramar hukumar Bebeji, kimanin kilomita 50 daga Kano, a yayin da ya rage ƙiris tawagar ta ƙarasa gida.
Tun a wancan lokaci, jama’a daga ciki da wajen Jihar Kano suka riƙa jimami da bayyana alhini, musamman duba da irin gudummawar da ’yan wasan suka bayar kafin rasuwarsu.