Gwamna ya zargi shugabannin APC da magudin zaben fid-da-gwani a Jihar Ogun
Gwamnan Jihar Ogun Sanata Ibikunle Amosun ya zargi wadansu shugabannin Jam’iyyar APC da shirya bita-da-kulli da zagon kasa a zaben fid-da-gwanin dan takarar Gwamna na Jam’iyyar APC a jihar. Gwamnan ya zargi uban Jam’iyyar APC ta Kasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas, Sanata Bola Ahmad Tinubu da tsohon Gwamnan Jihar Ogun Cif Segun Osoba da […]
Gwamnan Jihar Ogun Sanata Ibikunle Amosun ya zargi wadansu shugabannin Jam’iyyar APC da shirya bita-da-kulli da zagon kasa a zaben fid-da-gwanin dan takarar Gwamna na Jam’iyyar APC a jihar.
Gwamnan ya zargi uban Jam’iyyar APC ta Kasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas, Sanata Bola Ahmad Tinubu da tsohon Gwamnan Jihar Ogun Cif Segun Osoba da hada baki da Shugaban Jam’iyyar ta Kasa, Kwamared Adams Oshiomhole da shirya magudin zabe. Ya ce ba a yi zaben fid-da-gwanin dan takarar Gwamna na Jam’iyyar APC a Jihar Ogun ba.
“Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana sane da cewa babu zaben fid-da-gwani da Jam’iyyar APC ta yi a jihar, illa kawai wadansu mutane ne suka je Legas suka rubuta sakamakon zaben. Idan maganganun da na fada a kan Bola Tinubu da Segun Osoba ba haka ba ne su fito su musanta,” inji shi.
Gwamna Amosun ya fadi haka ne a ranar Litinin da ta gabata jim kadan da rantsar da Jojin Jihar, Mai shari’a Mosunmola Dipeolu, a Abeokuta. Ya furta kalaman cikin fushi, inda ya kalubalanci Bola Tunibu da Cif Osoba su fito fili su bayyana yadda aka kai ga samun sakamakon zaben.
Tirka-tirkar siyasa a tsakanin manyan jigogin Jam’iyyar APC ta fara kamari ne bayan zaben fid-da-gwani a jihar, inda bangaren jam’iyyar mai biyayya ga Gwamna Amosun ya fitar da sunan da dan takarar yake mara wa baya wato Adekunle Akinlade, yayin da bangare mai biyayya ga tsohon Gwamnan Jihar, Cif Olusegun Osoba ya fitar da sunan Dapo Abiodun; wanda shi ne shugabannin kwamitin shirya zaben na kasa suka ayyana, kum aka kai sunansa ga Hukumar Zabe ta Kasa. Tun daga wancan lokaci ne Gwamnan yake kokarin ganin ba a kai ga tabbatar da wannan dan takara ba. Domin a cewarsa, ba a gudanar da zabe ba.
Ko a karshen makon jiya Gwamnan da wadansu manyan sarakunan jihar sun ziyarci Shugaban Kasa; lamarin da ake dangantawa da dambarwar sakamakon zaben fad-da-gwani a jihar.
Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin bangaren da Gwamna Amosun yake zargi, amma lamarin da ya ci tura domin Cif Segun Osoba bai daga kiran wayar wakilinmu ba kuma bai amsa sakon tes da ya aike masa ba. Sai dai daya daga cikin jagororin ’yan Arewa da suke biyayya ga Cif Osoba, Hadi Sani ya shaida wa Aminiya cewa abin takaici ne ganin yadda Gwamna Ibikunle ya fito yana gutsiri-tsoma a kan zaben fid-da-gwanin. Ya ce hakan ba girmansa ba ne a matsayinsa na Gwamna kuma jigo a Jam’iyyar APC. Ya ce Dabo Abiodun ne zabin al’ummar jihar ba mutumin da shi Gwamnan yake so ya kakaba musu ba, don haka kamata ya yi ya nuna juriya da dattaku ya bar wa jama’ar jihar zabinsu.