Gwamna Yero: Gwarzon zaman lafiya

Kaduna gari ne da ya sha bambam da sauran garuruwan Arewacin kasar nan, shi ya sa ma ake masa kirari, ana cewa da shi garin gwamna, saboda kasancewarsa bariki na farko a yanki wanda ya kunshi dukkan kabilun kasar nan. Dangane da haka ne ake cewa  da mazauna garin Kaduna ka-zo-na-zo, domin kuwa yawan mazauna  […]

Gwamna Yero: Gwarzon zaman lafiya
Gwamna Yero: Gwarzon zaman lafiya

Kaduna gari ne da ya sha bambam da sauran garuruwan Arewacin kasar nan, shi ya sa ma ake masa kirari, ana cewa da shi garin gwamna, saboda kasancewarsa bariki na farko a yanki wanda ya kunshi dukkan kabilun kasar nan. Dangane da haka ne ake cewa  da mazauna garin Kaduna ka-zo-na-zo, domin kuwa yawan mazauna  garin ya  fi  na Gwarawa, ‘yan asalin garin da aka taras. Turawa ne suka kafa garin da niyyar zamantowarsa hedkwatar makekiyar Jihar Arewa wacce aka tsintsinka ta a yanzu zuwa jihohi goma sha tara.
Tun can fil-azal mulkin Arewacin kasar nan mawuyacin al’amari ne, kuma haka nan Turawa suka yi ta gwagwagwa da matsaloli daban-daban har ya zuwa lokacin da ‘yan kasa suka karbi mulkin daga hannunsu a karkashin Sardaunan Sakkwato, Sa Ahmadu Bello, Firimiyan farko kuma na karshe. Shi kansa Sardauna ma ya yi hakilo sosai wajen gudanar da mulkin Jihar Arewa daga garin Kaduna, ya kuma nuna cewa mulkin Arewa ba abu ne mai sauki ba, domin kuwa jama’ar da ake yi dominsu na cewa, “ba a iyawa, ba a gamawa, ba a yabawa.” To bayan wafatin Sa Ahmadu Bello da kuma kacancana daularsa da aka yi, sai Jihar Kaduna ta maye gurbin tsohuwar Jihar Arewar, ta kuma gaji dukkan matsalolin da aka yi ta fama da su a wancan lokacin da kuma hatsaniya da kataniyar kabilun Arewa fiye da 200 da suka yi kaka-gida a jihar.
Ko ba komai gwamatsuwar kabilu da yawa haka, masu mabambamtan addinai da dabi’u da al’adu, abu ne da ke haifar da matsaloli da wahalhalu ga mahukunta, musamman ma a harkokin da suka jibanci zaman lumana da fahimtar juna tsakankaninsu.
A kalla ba a kasara ba akwai kabilu dai-dai sama da 57 a Jihar Kaduna wadanda ke bin manyan addinai guda biyu. Ashe ke nan yanayin zamantakewar wadanan kabilu kan iya zamantowa mawuyaci, wanda kuma zai iya haifar da rigigimu da fitintinu iri-iri wadanda sai an yi da gaske a shawo kansu a duk lokacin da aka samu wata ‘yar matsala game da su.  Ba sai an fada ba jihar Kaduna na daga cikin jihohin da suka fi sauran fama da rikice-rikicen kabilanci da na addini a kasar nan, kuma gwamnonin da suka gabata sun yi iyaka kokarinsu wajen magance illolinsu.
A yanzu haka Gwamna Mukhtar Ramalan Yero ke kan karagar mulkin Jihar Kaduna, kuma tun daga hawansa sai ya fara daukan matakan da suka dace don kawar da abubuwan da ke haddasa rikice-rikice maimakon  yin fargar jaji, wato yunkurawa don yayyafa ruwa kan wutar da kan tashi. Ya nakalci irin dabaru da fasahar da gwamnonin da suka gabace shi, suka bi don kwantar da kurar dukkan rigingimun da suka taso, ya kuma gano yadda zai bi ya inganta su don a ji dadin dakile su tun kafin su kunno kai. Ya yi nazarin halayyar zamantakewar al’ummomin jihar Kaduna da yadda suke gudanar da harkokin zumuncin da ke tsakankaninsu da al’amuran da ke kawo tunzuri cikin  mu’amalolinsu da abubuwan da ke takura su, suke hana su yin hakuri da fahimtar wadanda addininsu ya sha bamban da na su.
Gwamna Ramalan Yero ya fahimci irin kata-katar da ta wanzu a  lokotan da aka yi ta fama da rigingimun addini da na kabilanci da kuma yamutsin siyasa a Jihar Kaduna; ya san dalilan afkuwarsu da kuma wadanda ke dada iza wutar ruruta su. Don haka ne yake taka-tsantsan a dukkan matakan da yake dauka don tabbatar da zaman lafiya da lumana mai dorewa a jihar  da ta fi kowacce wuyar mulki. A yanzu babu abin da Gwamna Yero ya fi mayar da hankalinsa akai kaman kokarin kade fitintinu irin wadanda suka sha afkuwa a Jihar Kaduna, kuma a duk inda ya je batunsa bai wuce na zaman lafiya, kuma dukkan abin da zai aikata sai ya auna shi bisa mizanin adalci don ya tabbatar hakan zai amfani jama’a ya kuma kara karfafa manufofinsa na tabbatar da lumana da kwanciyar hankalinsu.
A halin yanzu an fara fahimtarsa, an kuma gane inda ya dosa, jama’a na kuma alfahari da haka domin sun tabbata idan har suka agaza masa ya kai ga nasarar samar da dawwamammiyar zaman lafiya, zai samu sukunin shimfida adalcin da yake ta godo da  jami’an gwamnatinsa da sauran mahukuntar jihar su yi, sa’annan su kuma kamanta gaskiya a dukkan al’amuransu don fita kunyar talakawansu da kuma fushin Mahaliccinsu. Ba shakka ana iya cewa kwanciyar hankali da lumana sun kankama a karkashin mulkin Yero, kuma masu son tayar da tarzoma za su samu warki daidai kugunsu.