Gwamna Yero ya cika alkawarin gina gida ga dattijon da ya amince da allurar Foliyo

A ranar Litinin da ta wuce ne aka mika wa dattijon nan mai kimanin shekara 80, Malam Sa’idu Jibril makullan gidan da Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Mukhtar Ramalan Yero ya gina masa saboda amincewa da ya yi da allurar foliyo.Wata hudu da suka wuce ne Gwamnan ya ziyarci yankin Rigasa don kaddamar da allurar cutar […]

Gwamna Yero ya cika alkawarin gina gida ga dattijon da ya amince da allurar Foliyo

Malam Sa'idu a jikin sabon dakunan da Gwamna Yero ya gina masaA ranar Litinin da ta wuce ne aka mika wa dattijon nan mai kimanin shekara 80, Malam Sa’idu Jibril makullan gidan da Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Mukhtar Ramalan Yero ya gina masa saboda amincewa da ya yi da allurar foliyo.
Wata hudu da suka wuce ne Gwamnan ya ziyarci yankin Rigasa don kaddamar da allurar cutar foliyo inda a lokacin makwabcin dattijon ya ki amincewa Gwamna ya diga wa ’yarsa ruwan allurar.
Malam Sa’idu ya amince Gwamnan ya diga wa ’yarsa karama da jikokinsa allurar wanda jin dadin hakan ya sa Gwamnan ya yi alkawarin gina masa gida, kuma a ranar ce Gwamnan ya aika da wakilinsa ya ba dattijon makullan dakuna shida da ya gina masa.
Aminiya ta je gidan inda ta tattauna da Malam Sa’idu kan yadda yake ji game da wannan lamari, inda ya ce, “Gaskiya babu abin da zan ce da Gwamna sai Allah Ya saka masa da alheri. Domin ya cika alkawari da ya yi min. Na ji dadi sosai domin sun ce da ni ga makullan nan sun ba ni kuma wai idan na ga dama in shiga ko kuma in ba da haya domin gidana ne.”
Ya kara da cewa “Ya gina min dakuna shida ciki da falo-falo har uku. Sannan ga shi an jamin wutar lantarki sun sanya min wuta, domin a da ba ni da wutar lantarki a gidana. Allah Ya saka masa da alheri.”
Ya ce dama shi ba ya adawa da allurar poliyo amma mutane na nuna cewa allurar ba ta da kyau sai ga shi allurar ta zama alheri a wurinsa domin ya samu gida a sanadiyyar amincewa da ita.
“Dama ko matata ba ta nan da masu diga allurar sun zo ina ba da yara a diga musu. Idan kuma sun je makaranta ana diga musu. Sai ga shi yanzu abin ya zama mana alheri. Yadda ya yi min Allah Ya yi masa gida a Aljanna,” inji shi.
Ita ma uwargidan dattijon, Malam Sa’a cewa ta yi,”Mun huta da yoyon ruwan sama da sauro a dukunanmu domin a yanzu dakunan da suka gina mana masu fadi ne kuma na zamani. A yanzu ji nake kamar a Saudiya nake domin dakunan har da fanka da wutar lantarki aka saka mana. Gaskiya muna godiya ga Gwamna.”