Gwamna Yero ya gargadi masu son tada fitina
Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Mukhtar Ramalan Yero ya gargadi matasa masu niyyar lalata motoci da hotunan ’yan takarar PDP da kada su kuskura su fara domin duk wanda aka kama zai fuskanci fushin hukuma. Gwamnan ya ce, Jam’iyyar PDP tana matukar kaunar zaman lafiya amma duk wanda ya taba musu kaya ba zai ji da […]
Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Mukhtar Ramalan Yero ya gargadi matasa masu niyyar lalata motoci da hotunan ’yan takarar PDP da kada su kuskura su fara domin duk wanda aka kama zai fuskanci fushin hukuma.
Gwamnan ya ce, Jam’iyyar PDP tana matukar kaunar zaman lafiya amma duk wanda ya taba musu kaya ba zai ji da dadi ba.
Ya kuma bayyana wa magoya bayan jam’iyyar cewa duk wanda ya taba su, su taba shi, idan kuma ba za su iya taba shi ba, to, su sanar da hukuma.
Gwamna Yaro ya bayyana haka ne a lokacin kaddamar da kwamitin neman zabensa a Kaduna.
“Idan aka taba ku, ku kare kanku, idan kuma ba za ku iya ba, sai a sanar da mu domin mu kare ku. Akwai bukatar duk a zauna lafiya saboda haka bai dace ’yan siyasa su mayar da siyasa ta koma ko a mutu ko a yi rai ba, saboda Allah ke ba da mulki ga wanda Ya so a lokacin da Ya so. Duk masu kalaman batanci akwai bukatar su daina saboda babu wanda aka haifa da rikici ba kuma muna tsoron magana ba ne, sai dai kawai muna shiru ne saboda kasancewarmu shugabanni,” inji shi.
Ya kara da cewa’ “Za mu koya wa duk wanda yake ganin shi mai rigima ne yadda ake zama lafiya, idan kuwa ya ki za mu tabbatar da ya fuskunci fushin hukuma. Mun fara yakin neman zabenmu kuma a shirye muke mu ga wanda ya isa da zai kona mana motoci.”
Gwamnan ya yi kira ga jama’a su kasance masu bin doka da oda sannan ya shawarci duk ’yan takara da jam’iyyu su koma su wayar wa jama’a kai a kan abubuwan da suka dace su yi.