Gwamna Yero ya jajanta wa ’yan kasuwar Sabon Garin Zariya
Gwamna Mukhtar Ramalan Yero na Jihar Kaduna ya jajanta wa ’yan kasuwar Sabon Garin Zariya bisa gobarar da ta auka musu a karshen makon jiya, wanda ta kone rumfuna sama da 300 da asarar miliyoyin Naira. Gwaman ya yi hakan ne lokacin da ya ziyarci kasuwar, inda ya bayyana gobarar a matsayin wata masifa da […]
Gwamna Mukhtar Ramalan Yero na Jihar Kaduna ya jajanta wa ’yan kasuwar Sabon Garin Zariya bisa gobarar da ta auka musu a karshen makon jiya, wanda ta kone rumfuna sama da 300 da asarar miliyoyin Naira.
Gwaman ya yi hakan ne lokacin da ya ziyarci kasuwar, inda ya bayyana gobarar a matsayin wata masifa da ke faruwa ba tsammani. Ya ce: “Gwamnatin tuni ta sanya kasuwar da ta garin Kafancan cikin shirin ta na mayar da kasuwannin irin na zamani domin bunkasar harkokin kasuwanci fadin Jihar Kaduna.” Ya kuma yi alkawarin samar da na’ura bayar da wutan lantarki ga kasuwar ta yadda idan an tashi kasuwar za’a kashe wutar kamar yadda kungiyar ‘yan kasuwar ta bukata. Gwamnan ya kuma yi alkawarin bayar da tallafi ga ’yan kasuwar da su ka yi asarar dukiyar su da nufin rage musu radadi domin ci gaba da gudanar da kasuwancin su kamar yadda suka saba.
Tun farko Shugaban kasuwar Alhaji Abubakar Bagobiri ya bayyana cewa: “Muna kyautata zaton gobara ta faru ne a sanadiyyar matsalar wutar lantarki wadda aka kawo a cikin dare. Gobarar ta fi shafar bangaren ’yan nama da kifi da masu sayar da kayan marmari da masarufi da kuma wani sashe na masu sayar da zinare,” inji shi.