Gwamna Yuguda da Ministan Abuja sun sa zare
Gwamnan Jihar Bauchi Malam Isa Yuguda da Ministan Abuja Bala Mohammed sun sa zare a sakamakon ziyar da Shugaba Goodluck Jonathan ya kai Jihar Bauchi don yakin neman a kara zabensa a ranar 14 ga Fabrairu, 2015. A lokacin da shugaban kasa yake yakin neman zabensa a garin Bauchi a ranar Alhamis din makon jiya […]

Gwamnan Jihar Bauchi Malam Isa Yuguda da Ministan Abuja Bala Mohammed sun sa zare a sakamakon ziyar da Shugaba Goodluck Jonathan ya kai Jihar Bauchi don yakin neman a kara zabensa a ranar 14 ga Fabrairu, 2015.
A lokacin da shugaban kasa yake yakin neman zabensa a garin Bauchi a ranar Alhamis din makon jiya ne wadansu matasa rike da tsintsiya suka shiga filin taron mai suna Ibrahim Babangida Skuare, inda suka rika jifan rumfar da shugaban kasa da mukarrabansa suke da takalma da kuma robar ruwa.
Tun a ranar abin da ya faru Jam’iyyar PDP ta zargi ’yan Jam’iyyar APC da jifan shugaban kasa, amma jam’iyyar APC ta yi alla-wadai da wannan al’amari, sannan ta nisanta kanta da shi.
Wannan al’amari ya tayar da kura inda Gwamnan Jihar Bauchi Isa Yuguda ya wanke Jam’iyyar APC, sannan ya zargi wadansu mukarraban shugaban kasa mazauna Abuja da cewa su ne suka dauki nauyin abin da ya faru, don su nuna wa shugaban kasa cewa Yuguda ba komai ba ne, kuma al’ummar Jihar Bauchi ba sa sonsa.
Ministan Abuja Bala Mohammed ya karyata wannan batu, inda ya bayyana cewa ai Yuguda dan Jam’iyyar APC ne, domin kuwa har ware kudi ya yi don daukar nauyin ayyukan Jam’iyyar APC a Jihar Bauchi.
Gwamnan Jihar Bauchi ya ce babu hannun ’yan Jam’iyyar APC wajen jifan Shugaba Goodluck Jonathan, inda ya bayyana cewa wadansu ’yan siyasa daga Abuja ne suka shirya don a ci masa mutunci.
A wata hira da Gwamna Yuguda ya yi da sashen Hausa na gidan rediyon BBC ya ce an shirya makarkashiya ce don a nuna shi ba komai ba ne a Jihar Bauchi.
Gwamnan ya ce “Wadansu jiga-jigan jam’iyyarmu mazauna Abuja ne suka shirya wannan al’amari. Sun shirya hakan ne don su ci mini mutunci.”
Duk da cewa bai ambaci sunayen mutanen ba, amma an yi hasashen da Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Adamu Mu’azu da kuma Ministan Abuja Bala Mohammed yake.
Idan ba a manta ba Gwamna Yuguda ya samu sabani da Mu’azu da Bala Mohammed a baya, inda da kyar uwar jam’iyyarsu ta sasanta su.
“An shiya ne don a kunyata ni a gaban shugaban kasa.” Inji Yuguda.
“Al’amarin da ya faru cin mutunci ga Sarkin Bauchi da kuma ni, a matsayina na Gwamnan Jihar Bauchi. An kuma yi hakan ne don a kunyata mu a gaban Shugaba Goodluck Jonathan wanda ya kawo wa jiharmu ziyara, sannan ya ziyarci sarkin.
“A matsayin shugaban kasa na bakon sarki da kuma al’ummar Jihar Bauchi ya kamata mu karrama shi, mu kuma daraja shi, kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar, amma abin da matasan da ke rike da tsintsiya suka yi ba su kyauta ba.
Domin ya tabbatar da zargin da yake yi na cewa ’yan PDP ne suka jefi shugaban kasar ba wai ’yan APC ba, Yuguda ya kawo misali da ziyarar da Jonathan ya kai Jihar Kano, jihar da APC ce take da iko, amma ba a jefi shugaban kasa ba.
“Shugaban kasa ya kai irin ziyarar da ya kawo mana Jihar Bauchi, jihar da Jam’iyyar APC ke mulki, amma ya shiga duk wurin da yake so ba tare da an tsangwame shi ba. Ya ziyarci Sarkin Kano ma, kuma babu abin da ya faru. Me ya sa sai a Jihar Bauchi? Saboda suna so su nuna wa shugaban kasa ni ba kowa ba ne a jihata.”
A wata sanarwa da Ministan Abuja ya fitar mai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa Nosike Ogbuenyi, ya ce: “Abin takaici ne a ce Gwamna Yuguda ya zargi Ministan Abuja da daukar hayar ’yan daba don su jefi shugaban kasa. Wannan abin kunya ne.”
Sanarwar ta ce wanke ’yan APC da gwamnan ya yi ya nuna karara cewa yana da alaka ta kut-da-kut da jam’iyyar APC. “Wato da daddare shi dan APC ne, amma da rana kuma dan PDP.”
Sanarwar ta ce gwamnan ya yi gaggawar yanke hukunci ba tare da bincike ba, sannan me ya sa a lokacin da yake jawabi a wurin kamfen din matasan ba su jefe shi ba?
A wata hira da Ministan Abuja ya yi da gidan rediyon Jamus ya bukaci Yuguda ya bayyana wa duniya dalilin da ya sa ya zama mai magana da yawun jam’iyyar APC, inda ya wanke ta daga zargin da ake yi mata.
Ya ce: “Yaya za a yi in jefi ubangidana, wanda shi ne ya mayar da ni komai a rayuwa? Yaya zan wulakanta wanda a dalilinsa nake samun abincin da nake ci? Duk mai hankali ya san hakan ba zai yiwuwa ba.”
Minsitan ya ce ba zai daina goyon bayan Jonathan ba, saboda ra’ayinsa na Najeriya ta kasance kasa daya, saboda shi ne mutumin da kasar nan take bukata sakamakon shirinsa na bunkasa ta.
Daga karshe ya bukaci jama’a su mayar da hankali wajen abin da zai samar da zaman lafiya a kasar nan, sannan a zabi PDP, a kuma yi watsi da maganganun da Gwamna Yuguda ya yi saboda ba su da tushe ballantana makama.