Gwamna Abba ya rantsar da sabbin ciyamomi 44 a Kano

Gwamna Yusuf ya buƙaci sabbin shugabannin su kasance masu gaskiya.

Gwamna Abba ya rantsar da sabbin ciyamomi 44 a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da sabbin Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 da aka zaɓa, ciki har da mace, mai suna Sa’adatu Salisu.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kano (KANSIEC), ta ce jam’iyyar NNPP ce ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi guda 44 a zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar.

Kazalika, NNPP ta samu nasarar lashe kujerun kansiloli guda 484 a dukkanin mazaɓun jihar.

Shugaban KANSIEC, Farfesa Sani Lawal Malumfashi, ya sanar da sakamakon zaɓen a daren Asabar.

KANSIEC ta bai wa waɗanda suka yi nasara takardar shaidar lashe zaɓen a ranar Lahadi.

Bayan bikin rantsarwar, Gwamna Yusuf ya shawarci sabbin shugabannin da su zama masu adalci, su zama abin koyi, kuma su kasance masu sadaukarwa ga al’ummarsu.

Ya gode wa jama’ar Kano bisa yadda suka fito suka yi zaɓe.

Sannan ya buƙaci sabbin shugabannin su mayar da hankali wajen samar da ayyukan da za su tallafa wa ɓangaren ilimi, aikin gona, lafiya, da kuma buƙatun mata.

Gwamna Yusuf, ya kuma shawarci shugabannin su inganta sakatariyarsu ta ƙananan hukumomi, sannan su yi aiki tare da mutane daga kowane ɓangare na siyasa.

Ya tabbatar wa sabbin ciyamomin goyon bayan gwamnatinsa, tare da jaddada muhimmancin jajircewa wajen yi wa al’ummar Kano aiki.