Gwamnan Abiya ka daina biye wa jita-jita sai ka tantance gaskiya – Limami

Babban Limamin Masalalcin Aba da ke Jihar Abiya, Alhaji Bashir Idris ya shawarci hukumomin jihar, wadanda suka hada da Gwamna Theodore Orji da su rika kokarin tantance gaskiyar lamari kan jita-jitar da aka kai musu game da ’yan Arewa, kafin su kamasu, don gudun bata suna.A ganawar da ya yi da Aminiya bayan an sako […]

Gwamnan Abiya ka daina biye wa jita-jita sai ka tantance gaskiya – Limami
Gwamnan Abiya ka daina biye wa jita-jita sai ka tantance gaskiya – Limami

Babban Limamin Masalalcin Aba da ke Jihar Abiya, Alhaji Bashir Idris ya shawarci hukumomin jihar, wadanda suka hada da Gwamna Theodore Orji da su rika kokarin tantance gaskiyar lamari kan jita-jitar da aka kai musu game da ’yan Arewa, kafin su kamasu, don gudun bata suna.
A ganawar da ya yi da Aminiya bayan an sako shi, tare da wawsu ’yan Arewa mutum 11 da sojoji suka tsare su tare, bisa zargin sun boye makamai a masallaci, Babban Limamin y ace: Muna sane da cewa suna bibiyar harkokin tsaro, amma zai fi kyau su rika tantance gaskiyar lamari, ta hanyar tuntubar shugabannin al’ummar Arewa, tunda mu shugabanni za mu iya bayyana wa gwamnati gaskiya, don gudun kada aka wa wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, farmaki.”
Ya ce kimanin sojoji 50 ne suka far musu a masallaci, bayan da aka yada jita-jita cewa, sun boye makamai a masallaci, inda aka kama shi tare da mutum 13, sannan aka sake shi tare da mutum 11 bayan an tuhume su an tsawon sa’o’i 13. A cewarsa, har yanzu akwai saurna mutu biyu da sojoji ke tsare da su.
Sojojin sun binciki gidan limamin, da ba su samu komai ba, sai suka wuce da shi bariki, inda suka tsare shi har karfe ukun dare, sai washegari suka sake shi, kamar yadda ya bayyana.
“Sojojin sun ziyarci wuraren da mutanenmu ke zaune, wadanda suka hada da Lamba 92 da ke titin Hospital Road da Lamba 32 kan titin St. Michael, inda suka kama wani shugaban al’umma, amma da suka bincike su ba su samu komai na laifi ba,” inji shi.
A cewarsa, sojojin sun shiga dakin binciken kimiyya na wata makarantar sakandare mai zaman kanta, mallakar ’yan Arewa, inda suka kwace wasu sinadaran binciken kimiyya, inda suka doge da cewa, da su ake hada bom. Sannan sun kama mai makarantar da shugaban makarantar, wato AbdulRaheem Sani da AbdulMagidi Abubakar, wadanda har yanzu suke a tsare.
Sauran wuraren da sojojin suka kai samamen har da kasuwar shanu ta Lobanta, bayan gama yi musu tambayoyi ne  aka sako su washe gari Litinin.
Limamin  wanda yana daya daga cikin wadan da aka kama yayiwa Aminiya Karin bayani game da kama su da sako sun da aka yi  “ An sako mu bayan da suka tafi damu ofishin su dama kuma mu 13 ne sauran mutum biyu na hannun su suna ci gaba da tsare su” Ko bisa wane dalili ne sukayi awon gaba daku malam Bashir yaci gaba da cewa “ zargi ne dai mara tushe balle makama game da jita-jita da aka yada masu wai muna tara makamai a masallaci babu wani dalili da suka bamu gaskiya” injishi.