Gwamnan Akwa Ibom ya kori duk Kwamishinoninsa

Daga wurina, idan za a canza ku bisa rashin aiki, ina tsammanin babu wani Kwamishina da zai tafi.

Gwamnan Akwa Ibom ya kori duk Kwamishinoninsa

Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya sallami duk Kwamishinoninsa, ya ce ya yi hakan ne don buƙatar kawo sabbin mutane a cikin gwamnatinsa.

Da yake bayani yayin a taron bankwana da Kwamishinonin a ɗakin taro, ranar Juma’a, Eno ya ce babu ko ɗaya daga cikin Kwamishinonin da bai yi aiki tuƙuru ba.

Gwamnan wanda ya bayyana cewa, duk da cewa dukkansu sun sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, amma sai an sauya su domin a kawo sabbin ƙwararru a cikin gwamnatin.

“Daga wurina, idan za a canza ku bisa rashin aiki, ina tsammanin babu wani Kwamishina da zai tafi. Dukkan ku kun cika aikin ku kuma shi ne dalilin da ya sa ajandar gwamnatin tayi nasara. Amma dole ne mu kawo ƙarshen wannan rukunin, mu sake da wasu kuma mu ci gaba da gudanar da aikinmu, ”in ji shi.

Ya ce, za a gudanar da liyafar cin abincin dare ta bankwana a ranar Juma’a da yamma a ɗakin taro na Banquet Hall, da ke gidan gwamnati, Uyo, domin karrama Kwamishinonin da aka sallama.

Yawancin Kwamishinonin sun shafe kusan shekaru 10 suna aiki a yayin da wasu daga cikinsu suka yi aiki a ƙarƙashin tsohon Gwamna Udom Emanuel.