Gwamnan Anambra Ya Soke Harajin Masu Talla Da Walda

Mun cire su ne daga jerin masu biyan haraji saboda talakawa ne.

Gwamnan Anambra Ya Soke Harajin Masu Talla Da Walda

Gwamnan Jihar Anambra Farfesa Charles Soludo, ya yi amai ya lashe kan harajin da ya sanya wa masu sana’ar tura Wilbaro da talla a hanyoyi hadi da masu Walda a jihar.

A baya dai gwamnan ya ba da umarnin fara karbar harajin ne a matakan farko na fadada hanyoyin samun kudaden shiga, da a ka gudanar a gidan Gwamnatin Jihar da ke birnin Awka.

A cewarsa, masu tallan da masu tuka Amalanke, hadi da masu Bakaneza da sauran kananan sana’o’i, an hana su biyan haraji, tare da  jaddada cewa ya zamo dole a yada sakon ya je kunnen dukkan kasuwannin Anambra.

“Wadannan mutanen mun cire su ne daga jerin masu biyan haraji, saboda talakawa ne, don haka kada wanda ya karbi kudi a hannunsu.

“A isar da sakon nan ga duka kungiyoyin kasuwanni, domin duk wanda a ka samu ya karya wannan dokar, za a rushe kungiyarsa da karfin gwamnati ba tare da bata lokaci ba.

“Muna so ne  mu samar da yanayi da talakawa za su jajirce wajen sana’o’insu, domin rufa wa kansu asiri, ba wai mu matsa musu ba,” in ji shi.