Gwamnan Babban Banki ya yaba da tsarin aikewa da kudi na ‘Glo d change’
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Mista Godwin Emefiele ya yi nuni da cewa, tsarin aikewa da kudi na Glo dchange da aka kaddamar a Legas, cikin makon jiya,ci gaban kullin alaka ne tsakanin cibiyoyin hada-hadar kudi da kamfanonin sadarwa.A wata sanarwa da ya sanya wa hannu, game da samar da wannan kafa, ya taya kamfanin sadarwa […]

Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Mista Godwin Emefiele ya yi nuni da cewa, tsarin aikewa da kudi na Glo dchange da aka kaddamar a Legas, cikin makon jiya,ci gaban kullin alaka ne tsakanin cibiyoyin hada-hadar kudi da kamfanonin sadarwa.
A wata sanarwa da ya sanya wa hannu, game da samar da wannan kafa, ya taya kamfanin sadarwa na globacom murnar kaddamar da tsarin aikewa da kudi na “Glo dchange”, inda ya ce wannan nasara ce ga daukacin masu ruwa da tsaki.
Kamfanin sadarwa na Globacom tare da hadin gwiwar cibiyoyin hada-hadar kudi uku masu lasisi ke tafiyar d atsarin, kuma cibiyoyin sun hada da “FirstMonie da Bankin Eco da Bankin Stanbic IBTC, wadanda suka taru Jihar Legas ramnar Alhamis din makon jiya don kaddamar da shirin.
Shugaban Sashen Ciniki na Kamfanin Globacom, Mista Kamal Shonibare, ya ce tsarin aikewa da kudi na “Glo dchange” zai bayar da dama ga cibiyoyi aikewa da kudi su samar da wakilai a layukan sadarwarsu da ke daukacin fadin kasar nan, da kuma fasahar sadarwar da ake bukata don aikewa da sakonnin kudi ba tare da wata matsala ba.
Ya ce wannan tsarin zai bai wa bankunan da suka yi hadin gwiwar wajen aiwatar da shirin tare da kamfanin cin gajiyar kafofin sadarwar glo150 a daukacin fadin duniya da kantuna, wadanda suka zarta dubu 35 na dillalan glo, tare da kananan dilallai fiye da 400 da suka bude ofisoshinsu a gidajen main a ‘Con oil’ da ke fadin kasar nan.
Shonibare ya ce hadin gwiwar bankuna da Kamfanin sadarwa na Globacom, wani shiri na tabbatar da cewa kudi sun isa ga dimbin al’umma a daukacin fadin kasar nan, ta hanyar amfani da tsarin hada-hadar kasuwanci, wajen kulla alaka da abokan hulda, don rarraba kudi a daukacin fadin Najeriya.
Shi kuwa Darakatan Bankin Stamnbic IBTC, Mista Obinna Abajue da yake jawabi a madadin bankinsa, cewa ya yi, muna alfahari da kulla dangantaka da Globacom, domin “Glo ya samar da tsarin cike gibi da zai tabbatar da cewa kowa ya shigo ana damawa da shi a Najeriya wajen hada-hadar kudi.”
Kimanin shekara 11 da ta gabata, tun farko kafuwar Kamfanin sadarwa na Globacom ya ke ta bullo da shirye-shirye da ke inganta harkokin kasuwanci a Najeriya, wadanda suka hada da tsarin biyan kudi a kan kowace dakika na kiran waya da samar da alakar sadarwar intanet na tafi-da-gidanta (Mobile intanet) da bankin tafi-da-gidanka (M-) da tsarin amfani da layin glo a kasashen waje, wato abin da aka yi wa lakabi da ”Prepaid Roaming” da makamantansu.