Gwamna Bala Mohammed ya koma Jam’iyyar APM

Tuni Gwamna Bala ya karbi katinsa na zama mamba a sabuwar jam’iyyar a yayin taron da aka gudanar a yammacin Asabar.

Gwamna Bala Mohammed ya koma Jam’iyyar APM

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya sauya sheka zuwa Jami’iyyar APM bayan ficewarsa daga PDD.

A yammacin Asabar din nan ne gwamnan ya goranci jiga-jigan Jam’iyyar PDP a Jihar Bauchi suka sauya sheka zuwa APC bayan tattauna wa jagorrin APM a Jihar.

Taron masu ruwa da tsakin ya samu halarcin zababbun ’yan Majalisar Wakilai da Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Bauchi da Shguabannin Kananan Hukumomi 20 da shugabannin PDP Reshen Jihar daga Tsagin Tanimu Turaki da sauran masu ruwa da tsaki.

Tuni ya riga ya karbi katinsa na zama dan sabuwar jami’iyyar ta APM, a wani lamari da ya kasance kamar ba-zata.

Gwamna Bala ya bayyana cewa matakin da ya dauka na da matukar muhimmanci domin samun jam’iyya mai inganci da nufin hidimta wa al’umma, yana mai cewa sai da suka yi zuzzurfan tunani da tuntuba kafin komawarsu APM, bayan sun samu gamsuwa da ita.

Gwamnan ya bayyana cewa sabon matakin siyasa zai mai da hankali kan tattara magoya baya, ƙarfafa tsarin jam’iyya, da kuma gabatar da wata hanya mai inganci a zaɓe na gaba. Ya roƙi magoya bayansa da su kasance masu nutsuwa, haɗin kai, da mayar da hankali, tare da shiga cikin jama’a ta hanyar bayyana hangen nesa na jam’iyya da kuma jajircewarta wajen kyakkyawan mulki.

Sauya shekar tasa zuwa ne jima kadan bayan gwmanan ya sanar da cewa saura kiris ya sanar da jam’iyyar da zai koma bayan Kotun Koli ta soke babban taron PDP na kasa da ya sa jam’iyyar ta koma babu Kwamitin Gudanarwa na Kasa, ragamarta ya koma hannun Kwamitin Amintattu.

Bayan haka ne gwamnan ya sanar cewa ya zama wajibi su nemi mafita, domin samun damar shiga zaben 2027 da ke kara matsowa.

Tun da farko, Gwamna Bala, wanda ya bayyana aniyarsa ta tsaya takarar Sanatan Bauchi ta Kudu ya sanar da cewa yana tattaunawa da jagororin jam’iyyun adawa domin yanke hukunci kan jam’iyyar da zai koma.

Jim kadan kafin sauya shekar tasa, ya sanar da cewa yana tattaunawa da tsohon dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar NNPP a zaben 2023 kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso da takwaransa na Jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, wadanda su biyun ke neman takarar shugaban kasa da mataimaki a jam’iyyar ADC.

Sai dai kuma tuni rahotanni masu karfi suka bayyana cewa Kwankwaso da Obi za su koma sabuwar Jam’iyyar ADC. Injiniya Buba Galadima, wanda na hannun daman Kwankwaso ne, ya sanar da cewa a ranar Litinin manyan ’yan siyasar za su koma NDC.

A baya, tawagar Jam’iyyar ADC karkashin jagorancin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ta ziyarce shi ga Gidan Gwamnatin Bauchi bisa umarnin shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata David Mark, domin shawo kansa ya koma ADC. Bayan ganawar, Gwamna Bala Mohammed ya bayyana ADC a matsayin jam’iyyar da zai fi so ya koma idan har ya bar PDP.

Daga bisani, gwamnan ya yi wata ganawa da Shugaban Kasa Bola Tinubu da wasu manyan jagororin APC. Bayan nan, Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda, ma ya jagorance shi a Bauchi domin lallashinsa.

Sai dai tattaunawar ta rushe saboda rashin jituwa kan yadda za a raba ikon jam’iyyar da sauran tsare-tsare. Shugaban bangaren PDP na jihar karkashin jagorancin Tanimu Turaki, Samila Adamu Burga, ya zargi APC da kin amincewa da tsarin siyasar gwamnan.