Gwamnan Bauchi ya bada tallafin shanu 3 da shinkafa ga Fursunoni
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, ya bada tallafin shanu 3 da buhunan shinkafa 20 ga fursunonin da ke gidan yarin Bauchi ta tsakiya don bikin ranar Dimokuradiyya. Gwamnan ya ziyarci fursunonin ne don yin murnar zagayowar ranar dimokuradiyya tare da su da kuma sanin irin kalubalen da fursunonin jihar ke fuskanta. Gwamna Bala, […]
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, ya bada tallafin shanu 3 da buhunan shinkafa 20 ga fursunonin da ke gidan yarin Bauchi ta tsakiya don bikin ranar Dimokuradiyya.
Gwamnan ya ziyarci fursunonin ne don yin murnar zagayowar ranar dimokuradiyya tare da su da kuma sanin irin kalubalen da fursunonin jihar ke fuskanta.
Gwamna Bala, ya jaddadawa fursunonin cewa, gwamnatin jihar a shirye take wajen magance matsalolin da fursunonin jihar ke fuskanta.