Gwamnan Bauchi ya gabatar da kasafin N465bn na 2025

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulƙadir  Mohammed, ya gabatar da ƙudurin kasafin kuɗi na shekarar 2025 na N465,850,248,317 ga Majalisar dokoki domin tantancewa.

Gwamnan Bauchi ya gabatar da kasafin N465bn na 2025

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulƙadir  Mohammed, ya gabatar da ƙudurin kasafin kuɗi na shekarar 2025 na N465,850,248,317 ga Majalisar dokoki domin tantancewa.

Da yake gabatar da ƙudirin kasafin kudin, gwamnan ya ce abubuwan da ke cikin kasafin sun yi daidai da yanayin halin da tattalin arziki ke ciki a halin yanzu.

Gwamnan ya ce N182,743,955,931.60 (39.3%) na kasafin an ware su ne domin ayyukan yau da kullum, sai N282,341,322,385 (52%) kuma don manyan ayyuka.

Ya ce an ware wa ɓangaren gudanarwa N69,941,674,429.6, ɓangaren tattalin arziki N219,506,601,771.75, sai N9,538,142,748.76 na fannin shari’a, yayin da N166,098,829,366.96, aka ware kyautata rayuwar jama’a.

Gwamna Bala ya ce kasafin kudin ya zarce na 2024 da kashi 18 bisa 100 don aiwatar da biyan sabon tsarin fansho da na mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000.

A cewarsa, gwamnati za ta tabbatar da kammala dukkan ayyukan da ake gudanarwa don bude tattalin arzikin jihar.

Gwamna Bala ya ce hauhawan farashin da ke qara sa kaya tsada ya kuma shafi ayyuka da shirye-shiryen gwamnatin sa.

Shugaban majalisar Dokoki na Jihar Bauchi Alhaji Abubakar Yakubu Suleiman ya yi alƙawarin majalisar za ta yi aiki a kan dokar kasafin kudin a kan lokaci.

Ya yaba wa Gwamnan bisa gabatar da kasafin a kan lokaci.

Sai ya ce “Muna kira ga shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnati, da su zo su kare kasafin kudinsu, duk wanda ya ƙi zuwa ina tabbatar da cewa za a sanya masa takunkumi.”

Suleiman ya godewa Gwamnan bisa yadda yake ba da fifiko ga bukatun jama’a ta hanyar manufofinsa da shirye-shiryensa.

Tags