Gwamnan Bauchi ya nada Sakataren Gwamnati da wasu

Gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir Mohammed ya rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG) Alhaji Mohammed Sabiu Baba, da shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Alhaji Abubakar Kari  da Mataimakin shugaban ma’aikatan  Alhaji Bashir Ya’u. Gwamnan ya rantsar da su ne a yau Litinin a gidan gwamnatin jihar na Banquet Hall, Mai shari’a Rabi Talatu Umar […]

Gwamnan Bauchi ya nada Sakataren Gwamnati da wasu

Gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir Mohammed ya rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG) Alhaji Mohammed Sabiu Baba, da shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Alhaji Abubakar Kari  da Mataimakin shugaban ma’aikatan  Alhaji Bashir Ya’u.

Gwamnan ya rantsar da su ne a yau Litinin a gidan gwamnatin jihar na Banquet Hall, Mai shari’a Rabi Talatu Umar wanda ta wakilci babban Alkalin jihar Ahmed Mohammed Kabir Madaki ce, ta rantsar da sabbin nade-naden da Gwamnan ya yi.