Gwamnan Bauchi ya sallami Kwamishinoninsa
Gwamna Bala Abdulƙadir Mohammed na Jihar Bauchi ya sallami biyar daga cikin Kwamishinoninsa.
Gwamna Bala Abdulƙadir Mohammed na Jihar Bauchi ya sallami biyar daga cikin Kwamishinoninsa.
Kwamishinonin suka rasa kujeru su su ne:
- Dakta Jamila Muhammad Dahiru – Ilimi.
- Barista Abubakar Abdulhameed Bununu – Tsaro.
- Kwamred Usman Danturaki – Yaɗa Labarai.
- Farfesa Simon Madugu Yalams – Noma.
- Alhaji Yakubu Ibrahim Hamza – Addinin.
A ranar Litinin Gwamnan ya sanar da sallamar su tare da mika sunan wasu mutum takwas da yake son naɗawa a matsayin kwamishinoni a wani sabon garambawul da ya yi gwamnatinsa.
Ga jerin sunayensu da ƙananan hukumomin da suka fito:
- Hon. Isa Babayo Tilde – Toro
- Dakta Mohammed Lawal Rimin -Toro.
- Abdullahi Mohammed – Misau.
- Dakta Bala Musa Lukshi – Dass.
- Usman Usman Shehu – Shira.
- Iliyasu Aliyu Gital – Tafawa Ɓalewa
- Farfesa Titus Saul Ketkukah – Tafawa Ɓalewa.
- Hon Adamu Babayo Gabarin – Darazo.
Gwamnan ta hannun kakakinsa, Mukhtar Giɗaɗo ya ce an yi sauye-sauyen ne da nufin shigo da sabbin tunani wajen tafiyar da harkokin gwamnati domin ci gaban al’ummar Jihar Bauchi.
Kimanin wata guda ke nan da Sakataren Gwamnatin Jihar, Barista ya ajiye aikinsa, ba tare da bayyana dalili ba.
Tuni aka maye gurbinsa da tsohon Kwamishinan Kasafi da Tsare-tsaren Kuɗi, Aminu Hammayo.