Gwamnan Bauchi ya sallami mai ba shi shawara kan tsaro

Gwamnan ya umarce shi ya mika ragamar ofishin ga Babban Jami’in Tsaron Gwamnan.

Gwamnan Bauchi ya sallami mai ba shi shawara kan tsaro

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed

Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya sallami mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Dr Ahmed Adamu Chiroma, nan take.

Ya kuma umarci Ahmed Adamu Chiroma shi ya mika ragamar ofishin ga Babban Jami’in Tsaron Gwamnan.

An sanar da sallamar ce ta wasikar da sakataren gwamnatin jihar, Barista Ibrahim Mohammed Kashim ya sanya sanwa hamnu.

Sanarwar ta kuma gode wa tsohon mashawarcin gwamnan kan gudummawarsa ga gwamnati da al’ummar jihar.