Gwamnan Bauchi ya warke daga cutar Coronavirus

Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya warke daga cutar coronavirus bayan an fitar da sakamakon gwajinsa a karo na biyu. Gwamnan ya yi fiye da mako biyu yana jinya, tun ranar 24 ga watan Maris gwajin da aka yi wa Gwamnan ya nuna yana dauke da cutar Coronavirus. Da maraicen ranar Alhamis ne Gwamna Bala […]

Gwamnan Bauchi ya warke daga cutar Coronavirus

Gwamna Bala Mohammed ne mutum na farko da aka tabbatar ya kamu da cutar a jihar Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya warke daga cutar coronavirus bayan an fitar da sakamakon gwajinsa a karo na biyu.

Gwamnan ya yi fiye da mako biyu yana jinya, tun ranar 24 ga watan Maris gwajin da aka yi wa Gwamnan ya nuna yana dauke da cutar Coronavirus.

Da maraicen ranar Alhamis ne Gwamna Bala Muhammad Kaura, da kansa ne ya sanar da cewa gwajin da aka yi masa yanzu bai dauke da cutar, kamar yadda ya sanar a shafinsa na Twitter.

Gwamnan ya godewa masoyansa da suka saka shi a cikin addu’a lokacin da yake jinya. Sannan ya yaba da kokarin Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa NCDC tare da shugabannin addini na cikin jihar da wajen jihar.

 

Ma’aikatan Abuja ba sa sona — Wike

Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji da ofishin ’yan sanda

Gwamnati ta ƙara albashin sojoji — Ministan Tsaro

’Yan bindiga sun kashe mutum 3 a wani sabon hari a Filato