Gwamnan Bauchi ya yi wa matasa tanadi -Nasiru Umar
Shugaban Matasan Jam’iyyar APC ta Jihar Bauchi, Alhaji Nasiru wanda aka fi sani da Nasiru a kasa, a tsare ya bayyana cewa, gwamna ya yi tanadin inganta rayuwar matasan a kasafin kudin 2016.Matasan da suka yi wahala a lokacin zaben shugaban kasa da na gwamnoni, su kwantar da hankalinsu domin gwamnatin APC ta zo da […]
Shugaban Matasan Jam’iyyar APC ta Jihar Bauchi, Alhaji Nasiru wanda aka fi sani da Nasiru a kasa, a tsare ya bayyana cewa, gwamna ya yi tanadin inganta rayuwar matasan a kasafin kudin 2016.
Matasan da suka yi wahala a lokacin zaben shugaban kasa da na gwamnoni, su kwantar da hankalinsu domin gwamnatin APC ta zo da manufofi masu kyau na inganta rayuwar matasa da raya kasa, a cewarsa.
Nasiru ya kara da cewa, tabbas matasa sun bada gudunmawa wajen zaben Barista Mohammed Abubakar a matsayin Gwamnan Jihart Bauchi, saboda haka gwamna ya yi wasu tanade-tanade na musamman ga matasa nan da sabuwar shekara ta 2016.
“Kowa sai ya sha romon mulkin dimokuradiyya, amma a yanzu Gwamnatin Jihar Bauchi na fama da karancin kudi, sakamakon yadda jami’an tsohuwar gwamnatin suka yi ta wasoso da kudin al’umma,” inji shi.
Nasiru ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin wakilin Aminiya a ofishinsa da ke Bauchi da yammacin ranar Lahadin makon jiya.
Gwamna Abubakar ya gaji bashin albashin ma’aikata na watanni hudu, amma yanzu dukkan ma’aikatan da suke bin gwamnati bashi an biya su, sakamakon yadda aka toshe hanyoyin cuwa-cuwa da kudin al’umma.
A karshe ya shawarci magoya bayan jam’iyyar APC da su kwantar da hankalinsu nan da lokaci kadan kowa zai fara walwala. Domin a cewarsa, gwamnatin jiha za ta raba ayyuka yadda kowa zai amfana daidai gwargwado.