Gwamnan Bayelsa zai fitar da ’yan kwallo 22 zuwa Turai

Gwamnan Jihar Bayelsa Dickson Seriake ya kammala shirye-shirye don aikawa da kimanin ’yan kwallo 22 zuwa sassan Turai don samar musu kulob a can. Kafar sadarwar naij.com ta kalato cewa Gwamnan zai zakulo ’yan kwallon ne a wata gasar cin kofin da ya sanya da matasan za su fafata da ake wa lakabi da “Gasar […]

Gwamnan Bayelsa zai fitar da ’yan kwallo 22 zuwa Turai
Gwamnan Bayelsa zai fitar da ’yan kwallo 22 zuwa Turai

Gwamnan Jihar Bayelsa Dickson Seriake ya kammala shirye-shirye don aikawa da kimanin ’yan kwallo 22 zuwa sassan Turai don samar musu kulob a can.

Kafar sadarwar naij.com ta kalato cewa Gwamnan zai zakulo ’yan kwallon ne a wata gasar cin kofin da ya sanya da matasan za su fafata da ake wa lakabi da “Gasar cin kofin kwallon kafa na Dickson” wanda za a kwashe kimanin watannin biyu ana gudanar da ita. A karshen gasar ce za a zakulo matasan ’yan kwallon da suka fi hazaka inda zai tura su sassan Turai don samar musu da kulob.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da Matamakinsa Rear Adamiral John Jonah (mai ritaya) yake gabatar da jawabi a madadinsa a wajen bikin bude gasar. Ya ce matasa su ne kashin bayan kowace al’umma, don haka akwai bukatar a rika tallafa musu don ganin sun ciyar da kasar nan gaba a kowane fanni ciki har da na wasan kwallon kafa.
Ya ce Gwamnan ya yanke shawarar sanya kofin ne a karon farko da za a fara gasar cinsa a wannan shekara ta 2015 don karfafa gwiwar matasa su rungumi wasan kwallon kafa da hannu bibbiyu. Sai dai ya hori matasan da kada su yi sake da karatunsu, don haka su hada yin karatu da kuma wasan kwallon kafa don ganin sun jefi tsuntsaye biyu da dutse daya. Sai dai gasar za ta takaita ne a Jihar ta Bayelsa, inda ba ta karade daukacin kasar nan ba.
Tuni matasa daga yankuna daban-daban na jihar suka fara shirin shiga gasar don ganin an dama da su.
Sai dai Gwamnan ya kalubalance takwarorinsa Gwamnonin wasu jihohi da su yi koyi da shi wajen daukaka martabar wasan kwallon kafa na matasa don ganin ana zakulo matasan ’yan kwallo kuma ana fitar da su ketare don daukaka martabar Najeriya.

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram

An tsinci gawar wata mata babu kai a Abuja