Gwamnan Binuwai ya kori dukkan ma’aikatan da Ortom ya dauka yana dab da sauka

Ya kuma kori dukkan Manyan Sakatarorin da Ortom ya nada

Gwamnan Binuwai ya kori dukkan ma’aikatan da Ortom ya dauka yana dab da sauka

Gwamnan Jihar Binuwai, Hyacinth Alia

Gwamnan Jihar Binuwai, Hyacinth Alia, a ranar Laraba ya sanar da korar dukkan ma’aikatan da tsohon Gwamna Samuel Ortom ya dauka yana dab da sauka daga mulki.

Sabon Gwamnan ya kuma umarci sabbin Manyan Sakatarorin Jihar tare da umartar su da su mika ragama ga wadanda suka gada.

Umarnin dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kakakinsa, Tersoo Kula, inda ya umarci wadanda lamarin ya shafa su bi umarnin ba tare da bata lokaci ba.

Sanarwar ta ce, “Dukkan sabbin ma’aikatan da gwamnatin da ta gabata ta dauka tun daga farkon watan Mayu har zuwa yau, an soke daukar tasu.

“Dukkan wadanda lokacin ritayarsu ya yi amma ba su bar ofisoshinsu ba saboda an tsawaita musu shi, ana ba su shawara da su fara shirin tafiya.

“Kazalika, dukkan ma’aikatan da lokacin ritayarsu ya yi, amma ba su kai ga mika takardar ritayar tasu ba, da su ma su gaggauta yin hakan.

“Duk wani canjin wurin aiki ko ko sabon turi da aka yi wa ma’aikata daga watan Oktoban 2022 zuwa yau, shi ma an soke shi.”

A makon da ya gabata ne dai Alia na jam’iyyar APC ya karbi ragamar mulkin Jihar daga tsohon Gwamnan Ortom, wanda ya shafe shekara takwas yana mulkin jihar, a jam’iyyar PDP.

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!

Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru da kaso 33 a Najeriya — NBS

Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar rushe Hukumar EFCC

HOTUNA: Jana’izar tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa Lagbaja