Gwamnan Borno ya fusata kan karyata sace ’yan matan Chibok
Gwamnan Jihar Borno Alhaji Kashim Shettima ya nuna bacin ransa dangane da yadda wasu ke nuna kokwanto kan sace ’yan matan makarantar Chibok da ’yan Boko Haram suka yi garkuwa da su fiye da mako biyar da suka gabata.Gwamnan ya fadi haka ne a lokacin da Kwamitin Shugaban kasa domin binciko yadda aka sace ’yan […]
Gwamnan Jihar Borno Alhaji Kashim Shettima ya nuna bacin ransa dangane da yadda wasu ke nuna kokwanto kan sace ’yan matan makarantar Chibok da ’yan Boko Haram suka yi garkuwa da su fiye da mako biyar da suka gabata.
Gwamnan ya fadi haka ne a lokacin da Kwamitin Shugaban kasa domin binciko yadda aka sace ’yan mta ya ziyarce shi a Maiduguri a ranar Talatar da ta gabata.
Gwamna Shettima ya ce bai kamata a samu wani mai hankali da tunani da zai nuna kokwanto a kan wannan al’amari ba, kuma ya kamata a taya mu bakin ciki da damuwa da addu’ar Allah Ya kubutar da yaran, maimakon a karyata batun.
Ya ce maganganun da Shugabar Mata ta Jam’iyyar PDP Misis Kema Chikwe ta yi ko kadan bai kamata ba, “Wannan magana ce ta siyasa mu kuma ba siyasa muke yi ba, muna fadin abin da ya dame mu na batar yaran nan ne, a matsayinta na uwa idan ba za ta taimake mu da addu’a ko nuna damuwa da bakin ciki ba, bai kamata ta nuna kokwanto ba, ta bar mu mu ji da abin da ya dame mu,” inji Gwamnan.
Sai ya ce gwamnatinsa za ta ware Naira miliyan 150 don farfado da rayuwar ’yan mata 50 da suka kubuta daga hannun ’yan Boko Haram din da suka sace su.
Gwamnan ya kuma soki abin da ’yan bindigar suke yi, inda ya ce “Wadannan halaye nasu ba Musulunci ba ne, domin Musulunci bai koyar da kashe mutane ko kone dukiyar wanda bai san hawa ko sauka ba, balle yi masu yankan rago da sace su, ko don ba su bi akidarsu ba, domin babu tilastawa a cikin addini.”
Tun farko Shugaban Kwamitin mai wakilai 27, Birgediya Janar Ibrahim Sabo (mai ritaya), ya ce sun je jihar ce don ci gaba da aikin da aka dora masu. “Tun lokacin da Shugaban kasa ya dora mana wannan nauyi mako biyu da suka gabata muke ta kokarin ganawa da masu ruwa da tsaki a kan wannan al’amari a Abuja, bayan mun kammala ne muka yanke shawarar zuwa nan gindin magani don ganawa da jami’an tsaro da iyaye da malaman makarantar, tare da hada hannu da gwamnatin jihar don gano matsalar ta yadda za a magance ta,” inji shi.
Kwamitin ya ziyararci Mai martaba Shehun Borno Alhaji Abubakar Umar Garbai El-Kanemi, inda ya shaida musu cewa Jihar Borno jiha ce ta zaman lafiya, kuma al’ummar Borno ba su gaji irin wadannan fadace-fadace ba, baki ne suka shigo da wannan muguwar dabi’a da ta saba wa Musulunci. Ya roki al’umma su yawaita addu’o’i don kawo karshen wannan al’amari.