Gwamnan Dalta ya ja hankalin jama’a game da zabe
Gwamnan Jihar Dalta Dokta Emmanuel Uduaghan ya ja hankalin masu zabe na jam’iyyu daban-daban a jihar da cewa su guji duk abin da suka sani zai kawo tashin hankali a zabe kasar nan mai zuwa.Uduaghan ya bayyana hakan ne a wani taron da ya yi da ‘yan jari a garin Warri, inda ya ce ‘’Na […]
Gwamnan Jihar Dalta Dokta Emmanuel Uduaghan ya ja hankalin masu zabe na jam’iyyu daban-daban a jihar da cewa su guji duk abin da suka sani zai kawo tashin hankali a zabe kasar nan mai zuwa.
Uduaghan ya bayyana hakan ne a wani taron da ya yi da ‘yan jari a garin Warri, inda ya ce ‘’Na lura da akwai alamar yiwuwar marasa kishin kasa za su nemi tayar da fitina a zaben kasar nan, amma sai dai a ganina babu wata jam’iyya daya tilo da ta kamaci a mutu saboda ita, kuma babu wani zabe da za a ce ba a samun alamar fargaba a ciki, saboda irin wani yanayi da wani tsarin zabe zai fito a ciki na jefa tsoro a zukatan jam’a, amma idan muka yi amfani da hankali da kuma ilimin da Allah ya ba mu komai sai ya zo da sauki, duk da cewa shi zabe abu ne wanda ake ba da himma da karfi, amma ya kamata mu kwantar da hankulanmu akan abin da ya shafi kasar mu’’.
‘’Lallai mun tabbatar da cewa da dama mutane suna tsoron a yi tashin hankali a zabe, amma ya kamata mu sani a cikin jam’iyyun da muke da su gaba daya babu wata jam’iyya da ta fi rayuwarmu da zaman lafiyarmu da iyalanmu. Wannan ya fi komai muhimmanci. Don haka ya dace kowannen mu ya zama yana da hakuri da jama’a, domin shekara takwas da shekara hudu, ai za su zo. su wuce. Sai dai ina ganin zaben kasar nan yana son ya zama na addini alhali hakan ba daidai ba ne,” inji shi.