Gwamnan Doso ya hori al’ummar Jihar Kebbi kan allurar rigakafi
Gwamnan Jihar Doso da ke Jamhuriyar Nijar, Alhaji Sa’idu Jatau Ali ya bukaci jama’ar Jihar Kebbi su dauki allurar rigakafin shan-inna da muhimmanci domin kare ’ya’yansu daga kamuwa da cututtuka masu halaka kananan yara.Alhaji Sa’idu Jatau Ali ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabi ga dimbin jama’ar da suka halarci bikin […]
Gwamnan Jihar Doso da ke Jamhuriyar Nijar, Alhaji Sa’idu Jatau Ali ya bukaci jama’ar Jihar Kebbi su dauki allurar rigakafin shan-inna da muhimmanci domin kare ’ya’yansu daga kamuwa da cututtuka masu halaka kananan yara.
Alhaji Sa’idu Jatau Ali ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabi ga dimbin jama’ar da suka halarci bikin karrama Gwamnan Jihar Kebbi Alhaji Sa’idu Usman dakingari da wasu fitattun mutane da al’ummar karamar Hukumar Arewa Kangiwa suka shirya kan irin gudummawar da suka ba al’ummar karamar hukumar.
Gwamnan na Doso ya ce wasu lokuta iyaye kan ki yi wa ’ya’yansu allurar rigakafin cututtukan shan inna (shaushawa), wanda hakan yakan jefa su a cikin hadarin kamuwa da cututtukan da za iya magancewa idan sun yi musu allurar rigakafin.
Ya ce allurar rigakafi na kare yara daga kamuwa daga cututtukan tarin lala da karambau da kyanda da sauransu.
Gwamnan Doso ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta Jihar Kebbi su hada hannu da Nijar domin kula da baki masu shigowa kasashen biyu, saboda kare lafiyar al’ummarsu da dukiyarsu, inda ya ce Nijar da Najeriya danjumma ne da danjummai.
A jawabin Gwamna Sa’idu Usman Nasamu godiya ya yi ga al’ummar karamar Hukumar Arewa-Kangiwa kan wannan karramawa da suka yi masa da sauran wasu fitattun mutane.
Ya yi amfani da wannan dama inda ya kaddamar da saida takin zamani na bana a kan kowane buhu Naira 1,700, ya kuma ba shugabannin kananan hukumomi mako biyu cewa kowa ya tabbatar ya raba wa al’ummarsa takin domin kafin damina ta yi nisa.