Gwamnan Filato Ya Sa A kamo Wadanda Suka Kashe Makiyayi

Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya umarci jami’an tsaro da su zakulo wadanda suka kashe wani Bafulatani dan shekara 17 suka hallaka shanu 35 a Karamar Hukumar Barkin Ladi da ke jihar. Daraktan yada labarai na gwamnan, Gyang Bere, ya ce, dole ne a hukunta wadanda suka yi wannan danyen aiki, tare da tabbatar da adalci […]

Gwamnan Filato Ya Sa A kamo Wadanda Suka Kashe Makiyayi

Gwamnan Filato Caleb Muftwang

Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya umarci jami’an tsaro da su zakulo wadanda suka kashe wani Bafulatani dan shekara 17 suka hallaka shanu 35 a Karamar Hukumar Barkin Ladi da ke jihar.

Daraktan yada labarai na gwamnan, Gyang Bere, ya ce, dole ne a hukunta wadanda suka yi wannan danyen aiki, tare da tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa.

“Gwamna Caleb Mutfwang na alhinin harin da akai kai wa wannan Bafulatani da dukiyarsa, a tsakanin kauyen Nafan da ke gundumar Fan da Doruwa Babuje da ke Karamar Hukumar Barkin-Ladi.

“Mun sami labarin cewa wadanda suka aikata wannan aika-aika suna kan babura ne a lokacin da suka bude wuta kan wanda lamarin ya shafa, lamarin da ya kai ga mutuwarsa yayin da wani mutum kuma ya samu rauni.

“Gwamna Mutfwang, ya yi Allah wadai da wannan abu na rashin bin doka da oda, ya kuma ce wannan mummunan aiki na maida hanun agogo baya ga kokarin gwamnati na tabbatar da zaman lafiya a tsakanin kowa da kowa a jihar.

“Ya ce gwamnatinsa ba za ta ci gaba da hakuri ana yi wa jama’a kisan gilla ba.”

Gwamna Mutfwang ya umarci hukumomin tsaro da su binciko duk wani mai hanu a wannan mummunan laifi, tare da tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa.

Hakazalika ya bukaci shugabannin gargajiya da na addini, matasa da na mata da duk wadanda abin ya shafa, da su hada kai da sauran masu ruwa da tsaki su tattaunawa, domin a dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Zaɓen Edo: Yadda aka kama masu sayen ƙuri’a da ’yan daba

Sarakunan Nijar sun kai wa Gwamnatin Yobe ziyarar jaje

Ɗan majalisa ya yi jinjina kan naɗa Danyaya Sarkin Ningi

’Yan Sanda sun kama gungun ’yan fashi 7 a Katsina