Gwamnan Gombe: An dage shari’ar takarar Pantami zuwa watan Yuli
Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed da ɗage zaman kotun zuwa ranar 9 ga Yulin 2026 domin ci gaba da sauraron shari’ar.
Babbar Kotun Tarayya ta dage sauraron ƙarar da ke kalubalantar zaman Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ɗan takarar gwamnan jihar a Jam’iyyar PDP.
A ranar Litinin Babbar Kotun Tarayyar mai lamba ta 1 da ke zamanta a Gombe ta fara sauraron ƙarar da mai neman takarar gwamnan jihar a PDP, Abdulkadir Hamma Saleh ya shigar, yana ƙalubalantar tsarin da ya wa Pantami tikitin jam’iyyar.
Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed da ɗage zaman kotun zuwa ranar 9 ga Yulin 2026 domin ci gaba da sauraron shari’ar.
Abdulkadir Hamma Saleh yana neman kotun ta tantance sahihancin tsarin da ya haifar da zaɓen Pantami a matsayin ɗan takarar gwamna a PDP, yana mai zargin cewa an tafka kura-kurai da saba ƙa’ida wajen gudanar da zaɓen fid-da-gwani na jam’iyyar.
- ISWAP ta sace dalibai suna zana jarrabawar NECO a Borno
- Ba mu san an kama ’yan ta’adda sun dawo daga aikin Hajji ba — Gwamnatin Katsina
- ’Yan bindiga sun dasa bam a hanyar Sakkwato, sun kashe mutum ɗaya
A cewarsa, kafin ya garzaya kotu, ya gabatar da ƙorafe-ƙorafensa ga shugabannin PDP, yana mai buƙatar jam’iyyar ta duba yadda aka gudanar da zaɓen tare da warware matsalar ta hanyoyin sulhu na cikin gida.
Ya jaddada cewa amfani da hanyoyin sasanta rikice-rikicen cikin jam’iyya yana da muhimmanci wajen tabbatar da adalci, haɗin kai da bin ƙa’idojin da suka dace.
Sai dai bayan abin da ya bayyana a matsayin gazawar ƙoƙarin samun mafita daga cikin jam’iyyar, Saleh ya garzaya kotu domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen.
Ana sa ran shari’ar za ta ja hankalin masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa yayin da jam’iyyar PDP ke ƙara zage damtse wajen shirye-shiryen zaɓen Gwamnan Jihar Gombe na shekarar 2027.