Gwamnan Gombe ya rantsar da sabbin kwamishinoni 23
Yayin da wa’adin gwamnatin ya rage ƙasa da shekara guda, an umarce su fara aiwatar da manufofinta ba tare da ɓata lokaci ba.
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya rantsar da sabbin kwamishinoni 23, da sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar (HoS) da kuma masu ba shi shawara na musamman.
A wajen bikin rantsarwar da aka gudanar a Gombe ranar Asabar, gwamnan ya ce an zaɓi sabbin jami’an ne bisa la’akari da cancanta da kuma tabbatar da wakilcin dukkan ƙananan hukumomi 11 na jihar.
- Amurka za ta koyi darussan da ba za ta taɓa mantawa ba — Mojtaba Khamenei
- Sakkwatawa 9 sun rasu a hatsarin mota a hanyar Legas
Ya ce kasancewar wa’adin gwamnatinsa ya rage ƙasa da shekara guda, babu lokacin koyon aiki, don haka ya umarce su da su fara aiwatar da manufofin gwamnatin ba tare da ɓata lokaci ba.
Gwamnan ya buƙace su da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, riƙon amana da jajircewa, tare da kauce wa cin hanci da rashawa, amfani da mukami ba bisa ƙa’ida ba da duk wani abu da zai zubar da mutuncin gwamnati.
Ya kuma yaba wa manyan sakatarorin ma’aikatun jihar bisa yadda suka ci gaba da tafiyar da harkokin gwamnati tun bayan rushe Majalisar Zartarwa ta jihar a watan Afrilu na 2026.
Daga cikin sabbin kwamishinonin akwai Abdulkadir Mohammed Waziri (Noma da Tsaron Abinci), Farfesa Aishatu Umaru Maigari (Ilimi), Muhammad Gambo Magaji (Kuɗi da Bunƙasa Tattalin Arziki), Farfesa Danladi Adamu Bojude (Lafiya), Barrista Zubairu Muhammad Umar (Shari’a), Injiniya Bala Adams (Albarkatun Ruwa), Dakta Bertha Danja (Harkokin Mata) da Dakta Usman Maijama’a Kallamu (Ayyuka da Gine-gine).
