Gwamnan Imo ya ajiye mataimakinsa a zaben da yake namen zarcewa

Gwamnan ya maye gurbin mataimakin nasa da mace.

Gwamnan Imo ya ajiye mataimakinsa a zaben da yake namen zarcewa

Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodimma, ya ajiye mataimakinsa, Farfesa Placid Njoku, gabanin zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba.

Jerin sunayen da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fitar ya nuna cewa Uzodimma ya sauya sunan Placid da na mace, Misis Ekemaru Chinyere Ihuoma.

Haka kuma sunayen sun nuna cewar dan takarar jam’iyyar PDP, Samuel Anyanwu, ya zabi tsohon dan majalisar wakilai Jones Onyeriri a matsayin mataimakinsa.

Jam’iyyar LP tana da Sanata Athan Achonu a matsayin dan takarar gwamna tare da tsohon dan majalisar wakilai, Tony Nwulu, a matsayin mataimakinsa.

Masu sharhi kan al’amuran siyasa sun ce zaben mace a matsayin mataimakiya da APC ta yi, na nuni da son samun kuri’un mata a jihar.

Sun kuma bayyana cewa zabar Ekemaru, wanda ya fito daga yanki daya da dan takarar PDP, zai yi tasiri a zaben Nuwamba.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan