Gwamnan Jigawa Badaru shi ne shugaban kwamitin babban taron APC

Jam’iyyar APC a ranar Lahadin da ta gabata ta bayyana kafa kwamitin babban taronta inda Gwamnan Jigawa, Alhaji Abu-Bakr Badaru ya kasance shugaban kwamitin.   Sakataren shirye-shirye na jam’iyyar Sanata Osita Izunaso ya bayyana a kafar sadarwa ta jam’iyyar cewa kwamitin mai membobi 68 ya hada da Gwamnan jihar Imo da Barno da Oyo da […]

Gwamnan Jigawa Badaru shi ne shugaban kwamitin babban taron APC

Jam’iyyar APC a ranar Lahadin da ta gabata ta bayyana kafa kwamitin babban taronta inda Gwamnan Jigawa, Alhaji Abu-Bakr Badaru ya kasance shugaban kwamitin.
 
Sakataren shirye-shirye na jam’iyyar Sanata Osita Izunaso ya bayyana a kafar sadarwa ta jam’iyyar cewa kwamitin mai membobi 68 ya hada da Gwamnan jihar Imo da Barno da Oyo da Katsina da Yobe da Kaduna da Filato da Adamawa da Kogi da kuma jihar Edo.
 
Membobin kwamitin wadanda suka hada da sanatoci masu ci da tsofaffin sanatoci da wakilan majalisar tarayya da wasu fitattun shugabannin jam’iyyar sun hada da Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu da Sanata Ben Uwajumogu a matsayin mataimakin shugaba da kuma sakataren kwamitin.
 
Kamfanin Dillancin Labarai na NAN ya gano cewa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar su ne suka zabi Badaru bayan tattaunawa da shugabannin jam’iyyar suka yi a tsakaninsu.


Kofin Duniya: Jamus ta lallasa Curaçao da ci 7 a wasan farko

Mahaifinmu ba shi da ciwon suga – Ɗan Janar Rabe

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai