Gwamnan Jigawa ya dakatar da hadiminsa kan batun ƙarin albashi

Gwamnan ya dakatar da hadimin nasa har zuwa lokacin da kwamitin zai kammala bincikensa.

Gwamnan Jigawa ya dakatar da hadiminsa kan batun ƙarin albashi

Gwamnatin Jihar Jigawa, ta yi watsi da jita-jitar da ake yi cewar Gwamna Malam Umar A. Namadi, ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim ya fitar.

A cewarsa, labarin ba shi da tushe domin kwamitin da da gwamnatin ta kafa kan mafi ƙarancin albashi bai kammala haɗa rahotonsa ba.

Saboda haka, gwamnatin ta kafa sabon kwamitin da zai binciki tushen jita-jitar, da kuma dalilin da ya sa aka yaɗa ta.

Kwamitin zai kasance karkashin jagorancin Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Barista Bello Abdulkadir Fanini.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Kwamishinan Watsa Labarai, Sagir Musa Ahmed, Kwamishinan Lafiya, Dokta Muhammad Abdullahi Kainuwa, Babban Sakataren Tsare-Tsare da Ayyuka, Muhammad Yahaya Jabo, da Babban Sakataren REPA, Abba Mustapha Yola.

An bai wa kwamitin mako biyu don kammala bincikensa tare da gabatar da shi ga gwamnan jihar.

A halin da ake ciki, Gwamna Namadi ya dakatar da mai ba shi shawara kan albashi da fansho, Alhaji Bashir Ado Kazaure, har sai kwamitin ya kammala bincikensa.

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC