Gwamnan Jihar Oyo ya karya kwarin camfi game da maimai
Nasarar cin zaben kujerar Gwamna a zango na biyu da Gwamnan Jihar Oyo Sanata Isiaka Abiola Ajimobi, na APC ya samu a zaben da ya gabata ta sa ya zama Gwamna na farko da ya karya kwarin da wasu mutane ke yi cewa babu gwamnan da zai yi mulki sau biyu a wannan jiha. Sakamakon […]
Nasarar cin zaben kujerar Gwamna a zango na biyu da Gwamnan Jihar Oyo Sanata Isiaka Abiola Ajimobi, na APC ya samu a zaben da ya gabata ta sa ya zama Gwamna na farko da ya karya kwarin da wasu mutane ke yi cewa babu gwamnan da zai yi mulki sau biyu a wannan jiha.
Sakamakon zaben kujerar gwamna da wakilan majalisun dokoki na ranar Asabar da ta gabata da hukumar zabe ta bayar da yammacin ranar lahadi a Ibadan, ya nuna cewa, Gwamna dake kan gado, na jam’iyyar APC ne yayi nasarar samun kuri’u mafi rinjaye na 327,310. Tsohon Gwamnan jihar, Sanata Rasheed Ladoja na jam’iyyar Accord shi ne yazo na biyu da kuri’u 254,520. Shi ma tsohon Gwamna Adebayo Alao Akala na Labour yazo na uku ne da kuri’u 184,111 a yayin da Sanata Teslim Folarin na PDP yazo na hudu da kuri’u 79,019 sai Mista Seyi Makinde na SDP da yazo na biyar da kuri’u 54,740.
Da yammacin ranar Asabar da aka rufe rumfunan zabe ne Sanata Teslim Folarin, na PDP ya fito fili ya bayyana wa duniya cewa zai yi mubaya’a ga dukkan wanda ya lashe zaben wannan kujera ta Gwamna a jihar ta Oyo. Ya bayyana haka ne bayan ya samu sakamakon farko daga wakilansa a mazabu daban-daban dake nuna cewa an yi masa fintinkau.
Wani sabon abu da ba zaci zai iya faruwa ba shi ne, ’yan mintuna kadan kafin hukumar zabe ta bayyana sakamakon zaben a ranar Lahadi, sai tsohon Gwamna Adebayo Alao Akala na jam’iyyar Labour ya kira Gwamna Ajimobi ta waya yana taya shi murna. Amma Sakataren jam’iyyar Accord Dakta Nureni Adisa wanda ya wakilci jam’iyyar a wajen sauraron sakamakon zaben a harabar hukumar INEC ya ki sanya hannu ne a takardar da hukumar ta bayar ga wakilan jam’iyyu, wanda ya ce hedkwatar jam’iyyar Accord ce ta ba shi wannan umarni saboda zargin magudin zabe da ta ce an yi a mazabu daban-daban na jihar.
Sakamakon zaben da Farfesa Ayobami Salami ya karanta a gaban Kwamandodin tsaro na soja da ’yan sanda da kwastam da jami’an shigi-da-fici da wakilan jam’iyyu da ’yan jarida ya nuna cewa jam’iyyar APC ita ce ta lashe kujeru 18 na wakilan majalisar dokoki ta jihar. Ita kuwa jam’iyyar Accord ta samu lashe kujeru 8 ne, a yayin da jam’iyyar Labour ta samu kujeru 6.
Wakilinmu da ya zagaya sassa daban-daban na birnin Ibadan a ranar Asabar ya ce, babu mutane masu yawa da suka fito domin kada kuri’unsu a rumfunan zabe. Tabbatattun bayanai sun nuna cewa da yawa mutane sun ki fitowa ne saboda fargabar da suke yi cewa za a yi tashin hankali. Wasu mutanen da suka yi zamansu a cikin gidajensu sun yi wa wakilinmu bayanin cewa, zaben Shugaban kasa shi ne muhimmi gare su amma zaben gwamna da ’yan majalisar dokoki bai dame su. Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto babu wani labarin tashin hankali a birnin Ibadan da sauran garuruwa a jihar oyo.