Gwamnan Kaduna ya ɗauki nauyin karatun ɗaliban Kuriga
Gwamnan ya ce gidauniyarsa za ta ɗauki nauyin karatun daliban domin samun ingantaccen ilimi.
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi alkawarin bai wa ɗaliban Kuriga 137 da aka kubutar daga hannun ’yan bindiga tallafin karatu.
Gwamnan ya ce gidauniyarsa ta Uba Sani za ta gyara makarantun Kuriga domin bai wa yara a garin damar samun ingantaccen ilimi.
- Kisan Nafi’u: An sake gurfanar da Hafsat Chuchu a gaban wata Kotun
- Abubuwa 5 da ke hana waya saurin caji a lokacin zafi
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga daliban da suka kubuta daga hannun ‘yan bindiga a gidan gwamnatin jihar a ranar Alhamis.
Sani, ya ce bayan sako daliban, gwamnatin jihar ta dauki masana ilimin halayyar dan adam aiki wadanda suka shafe lokaci suna tattaunawa da daliban don tabbatar da lafiyarsu.
Sai dai ya bayyana cewar ɗaya daga cikin malaman da aka sace, mai suna Malam Abubakar ya rasa ransa sakamakon matsalar rashin lafiya.
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta dauki nauyin karatun ’ya’yan malamin da ya rasu, tare da bai wa iyalansa kyautar Naira miliyan 10.
Sani ya ce, “Jiya iyayen daliban sun zo nan, sun hadu da yaran, kowa ya yi murna. Ina so na yaba wa yaran. Sun yi hakuri da mu. Sun kuma fahimci halin da suka tsinci kansu a ciki.
“Lokacin da suka dawo, mun fahimci wasu na cikin matsanancin hali. Wannan shi ne dalilin da ya sa muka dauko masana ilimin halayyar dan adam, wadanda suka ba su shawarwari. Na yi farin ciki kamar yadda yaran suka yi farin ciki.
“Kwana biyu da kubutarsu, sun nuna ba sa son komawa gida, sun so zama da ni a nan na tsawon mako biyu. Amma na sanar da su cewar ba zai yiwu ba dole su koma gida. Iyayensu na muradin ganin su bayan shafe kimanin kwana 17 a hannun ‘yan bindiga.”
Gwamnan ya kara da cewa, “Na kuma bayar da umarnin yin gyare-gyare a garin da kuma makarantunsu, domin Kuriga na daya daga cikin gankuna mafi zaman lafiya a Kaduna.”
Gwamnatin Tarayya, ta musanta rade-radin da ake na cewar an biya kudin fansa domin sako daliban.