Gwamnan Kaduna ya ba mu umarnin biyan marayu hakkinsu amma…

Alkalin alkalan Jihar Kaduna, Dokta Maccido Ibrahim ya tabbatar da samun umarnin Gwamnan Jihar Alhaji Mukhtar Ramalan Yero kan a biya marayun da aka yi wa sama da fadi da kudin gadonsu kimanin Naira miliyan 22, daga asusun Kotun daukaka kara ta Shari’ar Musulunci, tunda daga wurinsu aka sami kuskure.  Dokta Maccido Ibrahim ya bayyana […]

Gwamnan Kaduna ya ba mu umarnin biyan marayu hakkinsu amma…
Gwamnan Kaduna ya ba mu umarnin biyan marayu hakkinsu amma…

Alkalin alkalan Jihar Kaduna, Dokta Maccido Ibrahim ya tabbatar da samun umarnin Gwamnan Jihar Alhaji Mukhtar Ramalan Yero kan a biya marayun da aka yi wa sama da fadi da kudin gadonsu kimanin Naira miliyan 22, daga asusun Kotun daukaka kara ta Shari’ar Musulunci, tunda daga wurinsu aka sami kuskure. 

Dokta Maccido Ibrahim ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da wakilinmu a Kaduna a ofishinsa ranar Talata. Sai dai ya koka kan rashin kudin da za a aiwatar da wannan umarni, kuma ya roki Gwamnan ya tallafa musu da kudin da za su samu damar biyan wannan kudi, ta yadda koda a kasafin kudinsu ana iya yankewa idan lokaci ya yi.
Alkalin Alkalan ya musanta cewa suna da masaniya kan lamarin tun asali, ya ce da sun sani da sun dauki matakin da ya dace ba za su yi shiru ba, balle su yi muku-muku ko rufa-rufa a watsar da shi ba.
Ya ce ya fara jin lamarin ne daga Babban Magatakardan Kotunan Jihar Kaduna, kafin magadan sun daukaka kokensu zuwa gare shi. “Da ya ji yadda lamarin ya gudana ma, sai da na nemi lallai alkalin Kotun Shari’a da ke Kawo ya fitar wa magadan hakkinsu ya biya su, musamman ma da aka yi ta gada-gada cewa ba ya da hannu a cikin kin ba su hakkinsu. Su magadan ne suka zo suka ce mini, wai alkali ya ce na ce ba za a ba su hakkinsu ba, sai an ba ni Naira miliyan biyu. Wannan ya sa na kira alkalin, ga ni ga su, na ce su maimaita abin da suka fada mini, na ce wa alkali, ‘Haka muka yi?’ Ya ce, a’a. Na ce, ‘To ka je ka biya su kudinsu’,” inji shi.
Alkalin alkalan ya ce ya tura batun alkalin da duk ma’aikatan da ke da hannun cikin lamarin ga Hukumar Shari’a ta Jihar (JSC) don ta dauki mataki a kansu.
A karshe ya zargi gidan rediyon Muryar Amurka da rashin bin ka’idar aiki ta fuskar rashin daidaita bincike dangane da lamarin tun farko don samun tabbatacciyar madafa.
Ya ce dan jarida kamar alkali ne, sai ya yi bincike kan al’amari sosai don ya tabbatar da gaskiyarsa kafin ya yanke wani hukunci. “Wannan shi ne abin da ya kamata su yi kafin su kai ga gabatar da abin da suke gabatar wa duniya, amma ba kame-kame da shaci-fadi ba”, inji Alkalin Alkalan.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi