Gwamnan Kaduna ya yi alkawarin kawo karshen satar shanu a jiharsa
Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Mukhtar Ramalan Yero ya sha alwashin kawo karshen satar shanu a fadin jihar. Gwamna Yero ya bayyana haka ne a lokacin da shugabannin kungiyar Miyetti Allah suka kai masa ziyara a gidan gwamnatin a ranar Talatar da ta wuce. Ya ce akasarin barayin shanun mutane ne da ke zaune a garuruwan […]
Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Mukhtar Ramalan Yero ya sha alwashin kawo karshen satar shanu a fadin jihar. Gwamna Yero ya bayyana haka ne a lokacin da shugabannin kungiyar Miyetti Allah suka kai masa ziyara a gidan gwamnatin a ranar Talatar da ta wuce. Ya ce akasarin barayin shanun mutane ne da ke zaune a garuruwan da ke kan iyakar jihar da wasu jihohin.“Satar shanu abu ne da ke damun mutane. Kuma Fulani da wadanda ba Fulani ba, sai zargin juna suke yi, saboda haka dole ne mu yi wani abu a kai domin ba Jihar Kaduna kawai abin ya shafa ba. Kuma dole ne mu tuntubi sauran jihohi makwabta domin samo hanyoyin magance matsalar,” inji shi. Gwamna Yero ya ce ga dukkan alamu akwai sa hannun wadanda ba ’yan kasar nan ba saboda a duk lokacin da aka yi satar, hanyar da suke bi hanya ce ta fita daga kasar nan. Gwamna Yero ya ce akwai bukatar Gwamnatin Tarayya domin ta sa hannu wajen kawo karshen matsalar saboda matsala ce da ta shafa jihohin Zamfara da Katsina da Kebbi da Nerja da sauransu. A jawabin shugaban kungiyar Miyatti Allah na Jihar Kaduna, Ardo Ahmadu Suleiman ya ce satar shanu ta zama wata matsala babba da ke damun Fulanin kasar nan, don haka ya yi kira ga gwamnati ta tashi tsaye wajen kawo karshen wannan matsala.