Gwamnan Kano Abba ya fara saka da mugun zare!

Duk wadanda suka bai wa Gwamnan Kano Abba shawarar fara wadannan rushe-rushe ba su kyauta masa ba.

Gwamnan Kano Abba ya fara saka da mugun zare!

Rusau din da aka yi a Kano a ranar Lahadi

Abin da yake faruwa a Jihar Kano na ruguje gine-gine da Gwamnatin Abba Kabiru Yusuf take yi babban abin kunya ne.

A halin da ake ciki Gwamna ya yi gaggawa da kuma saurin nuna fushinsa wajen rushe gine-gine a filayen da Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje da ta shude ta bayar da dama.

A bisa doka ta mallakar filaye, Gwamna shi ne yake da hakkin mallaka wa wani ko wasu filaye, haka kuma doka ta ba shi damar karbe wadannan filaye bisa dalilai, ita ma ba haka kurum ba.

Ga dukkan wanda yake bibiyar abin da yake faruwa a siyasar Kano, ya san akwai tsamin dangantaka mai tsanani a tsakanin Gwamnatin Ganduje da ta shude da kuma Gwamnatin Abba da take bisa kujera a yanzu.

Kusan tun kafin a rantsar da Abba a matsayin Gwamnan Kano ya soma fitar da takarda yana gargadin mutane a kan su daina gine-gine a wasu wurare da suke ganin Gwamna mai barin gado ya sayar a lokacin.

Wajen kuwa sun hada da jikin ganuwar birnin Kano da Masallacin Idi da ke tsakiyar birnin Kano da kuma wasu makarantu da ake ganin an yayyanka su an yi gine-gine a cikinsu, ko a wancan lokacin, sai da Gwamna mai barin gado Abdullahi Ganduje ya ja hankalin Gwamna mai jiran gado Abba ya sani cewa wa’adinsa a matsayin Gwamnan Kano zai kare ne a ranar 29 ga Mayun da ya gabata, don haka kafin lokacin a cewarsa, yana da ikon yin tasarrufi da duk abin da ya ga dama kamar yadda doka ta ba shi dama.

An sha samun sa-toka sa-katsi a tsakanin shugabannin biyu. Don haka za mu iya cewa wadannan abubuwa da suke faruwa na ruguje gine-gine, dama an yi tsammaninsu, sai dai abin ya zo da ba-zata, babu wanda ya yi tsammanin cewa za a wayi gari cikin dare an je an rushe ginin da tuni mutane suka fara kama haya suka zuba kayansu a ciki.

Kwatsam sai aka wayi gari Gwamna da kansa ya je wani katafaren gini da ke Titin Race course ya hau kan katafila aka ruguje ginin tare da shi, wanda kan ka ce kwabo labari ya bazu a kafafen sada zumunta, inda mutane suka yi tururuwa zuwa wajen, nan aka dinga satar kayan mutane babu ji babu gani kuma ido na ganin ido.

Akwai kurakurai sosai a kan matakin da Gwamnan Kano ya dauka na rushe wadannan gine-gine, kuma wannan alamu ne da suke nuna cewa ya soma saka da mugun zare, domin abin da ya kamata a ce ya yi, shi ne ya kafa kwamiti na kwararru, masana a harkar kasa da safiyo da kuma masana a harkar kasuwanci su ba shi shawara a kan yadda za a bullo wa wadannan wurare da suke ganin an yi kuskure wajen sayar da su.

Akalla abin da ya kamata Gwamnan ya yi ke nan, sannan ya ba su wa’adi takaitacce idan yana son abin da gaggawa, alabasshi sai ya duba ya ga abin da ya fi dacewa a yi a wuraren da ake ganin ba daidai ba ne a ce an gine su an mayar da su wajen kasuwanci.

Mun sani a bisa doka, Gwamna ko Ganduje ne ko ba shi ba ne, doka ta ba shi damar ya yanka filaye tunda kasa ta gwamnati ce, sannan a raba wa mutanen da za su iya gina wuraren.

Misali a lokacin da Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso yake Gwamnan Kano daga 1999 zuwa shekarar 2003, shi ne ya sayar da filayen da suke jikin ganuwar birnin Kano daga Kofar Kabuga zuwa BUK zuwa Kofar Dukawuya zuwa Kofar Famfo, wanda duk ya san wannan ya san a lokacin Kwankwaso yana Gwamnan Kano zangonsa na farko aka gina wajen.

Haka Makarantar ’Yan mata ta WTC da ke Kofar Famfo, ita ma Gwamnan ya yanke bayan makarantar aka fitar da filaye aka sayar wa mutane aka kirkiri sabuwar unguwa a wajen.

Bugu-da-kari, Kwankwaso yana Gwamna a zangon mulkinsa na farko ya yanke filin Makarantar GTC Gwale da GSS Gwale aka mayar da wajen filaye duk da yake har ya sauka ba a gina wajen ba.

Amma mun sani makarantar ’yan mata ta Goron Dutse da ke kusa da Makabartar Dandolo ita ma Kwankwaso ne ya yanke ta aka fitar da sabuwar unguwa a wajen, wadannan da wasu gurare da yawa tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ya yanke su aka mayar da su filaye aka yi gine -gine a wajen tuni wasu sun zama unguwanni na musamman.

Haka da Malam Ibrahim Shekarau ya zo a matsayin Gwamna, shi ma ya bayar da filaye a wurare da dama a Jihar Kano, tun da doka ta ba shi dama.

Shi ma Kwankwaso da ya sake dawowa a karo na biyu a matsayin Gwamnan Kano ya sake samar da sababbin filaye kuma an sayar da su mutane sun giggina kayansu, to, ta ina wanda Abdullahi Umar Ganduje ya yi ya zama laifi?

Shin laifi ne a matsayinsa na Gwamna ya yanka filaye? Wane irin laifi ya yi da magabatansa Kwankwaso da Malam Shekarau ba su yi ba na yanka filaye a sayar da su?

Ba muna magana ba ne a kan inda aka yanka ya zama fili ba, muna magana ne a kan shin doka ta bai wa Gwamna damar yanka filaye ko ba ta ba shi ba, kuma shin ta yaya shi sabon Gwamna Abba Kabiru ya gamsu cewa doka ta ba shi damar ya rushe ko’ina, amma bai gamsu irin wannan dokar ta bai wa magabacinsa Ganduje damar ya ba da wuraren a gina su ba?

Ai a bisa doka da ka’ida, idan ka sayi fili a wajen gwamnati ko aka ba ka, dole sai an bayar da abin da ake cewa satifiket, wato takardar mallakar wajen da kuma takardar iznin fara gini daga hukumar tsara birane ta jiha.

Duk mutane su cika wannan ka’ida amma a zo daga baya a ce abin da suka yi laifi ne don me za su sayi wajen?

A hakikanin gaskiya dukkan wadanda suka bai wa Gwamnan Kano Abba shawarar fara wadannan rushe-rushe ba su kyauta masa ba, kuma sun kai shi sun baro, domin ko shi Gwamnan Kaduna da ya yi nasa rusau din ai ba irin haka ya yi na rashin hankali ba.

Lallai ya kamata a ce Gwamnatin Kano ta ji kiraye-kirayen da ake mata na ta dakatar da wannan kudiri nata na rushe gine-gine ba tare da iznin kotu ba, kuma dukkan mutanen da suka cika ka’ida wajen gine-ginensu a biya su diyyar barnar da aka yi musu.

Haka kuma, wani abin takaicin da ya faru a sanadiyar wadannan rusherushe, shi ne, yadda matasa maza da mata suka zama barayi suna shiga suna dibar kayan mutane ana kallonsu.

Allah Ya kyauta.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna