Gwamnan Kano ya dauki Lauyan Tinubu ya yi wakilcin shari’arsa a Kotu

A watan da ya gabata ne Kotun Zabe ta ayyana Nasir Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben Kano.

Gwamnan Kano ya dauki Lauyan Tinubu ya yi wakilcin shari’arsa a Kotu

Wole Olanipekun (SAN)

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dauki hayar fitaccen lauyan nan, Cif Wole Olanipekun (SAN) domin ya wakilci shari’arsa a Kotun Daukaka Kara.

Aminiya ta ruwaito cewa a watan da ya gabata ne Kotun Sauraron Karar Zabe ta Jihar Kano ta sauke Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar, inda ta ayyana Nasir Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris.

Da yake kalubalantar hukuncin kotun, Abba Kabir Yusuf ya gabatar da korafi a gaban Kotun Daukaka Kara da hujjoji har guda 42, inda ya bukaci kotun ta yi watsi da hukuncin sannan kuma ta yi watsi da karar da APC ta shigar.

A kunshin karar da Abba Kabir Yusuf ya shigar, Aminiya ta lura cewa, Cif Wole Olanipekun (SAN), wanda ya jagoranci lauyoyin da su ka kare Shugaba Bola Tinubu a shari’ar zaben Shugaban Kasa tsakaninsa da Atiku Abubakar da Peter Obi, shi ne zai wakilci tasa shari’ar.

Haka kuma, a cikin tawagar lauyoyin Gwamna Abba akwai; Bode Olanipekun (SAN) da Ibrahim G. Waru da Akintola Makinde, yayin da Cif E.O.B. Offiong zai ci gaba da kasancewa lauyan na APC.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan