Majalisar Shura: Abba ya naɗa manyan malamai 46 a Majalisar Ƙoli

Gwamna Abba ya naɗa manyan malaman Musulunci 46 daga ɗariku daban-daban tare da ƙwararru daga fannoni daban-daban a matsayin majalisar ƙoli ta jihar Kano

Majalisar Shura: Abba ya naɗa manyan malamai 46 a Majalisar Ƙoli

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya kafa Majalisar Shura mai ɗauke da manyan malaman Musulunci da ƙwararrun domin ba shi shawara kan al’amuran mulkin jihar.

Gwamnan ya ba babbae majalisar shawa ta jihar ne kasa da awa 24 bayan ya sallami Sakataren Gwamnati ya rushe ofishin shugaban ma’aikatansa tare da sallamar kwamishinoni biyar.

Majalisar wadda za ta kasance ƙarƙashin jagorancin Farfesa Shehu Galadanci an kafa ta ne domin tafiya tare da kowane ɓangare da nufin ba wa gwamnan shawarwari ta fuskan addini da shugancin da sauran al’amuran da suka shafi al’ummar jihar.

Mataimakin Shugaban Majalisar Shura shin ne Farfesa Muhammad Sani Zahradeen.

Sanarwar ta da kakakin Gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa

ta bayyana ƙwarin gwiwar gwamnan game da zurfin ilimi da kuma kwarewar malaman wajen taimakawa domin kawo wa Kano ci-gaba ta fuskar addini da al’adu ta kuma tattalin arziki.

Mambobin Majalisar Shuran sun hada da: Sheikh Wazirin Kano, Malam Abdullahi Uwais, Sheikh Shehi Maihula, Farfesa Umar Sani Fagge, Sheikh Sayyadi Bashir Tijjani, Farfesa Muhammad Babangida, Sheikh Nasidi Abubakar Goron-Dutse da Khalifa Sukairaj Salga.

Sauran su ne: Sheikh Hadi Ibrahim Hotoro, Khalifa Tuhami Atiku, Sheikh Nasir Adam, Sheikh Muhammad Bin Othman, Sheikh Musal Kasiyuni, Dr. Muhammad Tahir Adamu, Sheikh Liman Halilu Getso, Malam Abdurrahman Umar, Malam Ado Muhammad Dalhatu, Abdullahi Salihu Aikawa, Dr. Nazifi Umar, Sheikh Abubakar Kandahar, Sheikh Umar Sanji Fagge da kuma Sheikh Sani Shehu Maihula.

Akwai kuma Malam Kabiru Dantaura, Sheikh Sammani Yusuf Makwarari, Khalifa Abdulkadir Ramadan, Malam Nura Adam, Malam Ado Muhammad Baha, Malam Nura Arzai, Malam Saidu Adhama, Malam Sani Umar R/Lemo, Gwani Ali Haruna Makoda, Sheikh Auwal Tijjani, Manjo-Janar Muhammad Inuwa Idris, Alhaji Sabiu Bako da kuma Alhaji Muhammadu Adakawa.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano