Gwamnan Kano ya raba wa makarantu kujeru da tebura 73,000
Gwamnan ya jadadda aniyarsa na ganin ilimi ya inganta a jihar.
A wani mataki na inganta harkar ilimi, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya raba wa makarantu da ke ƙananan hukumomi 44 na jihar, kujeru da tebura 73,800.
Wannan dai na daga cikin ƙoƙarin gwamnan na inganta harkar ilimi a Kano, bayan ƙaddamar da dokar ta-ɓaci kan Ilimi a baya-bayan nan.
- Zaɓen Edo: Duk wanda ya kaɗa ƙuri’a ya koma gida ya zauna — ’Yan sanda
- Hotunan yadda Zaɓen Gwamnan Edo ke gudana
Yayin ƙaddamar da dokar gwamnan, ya jadadda aniyarsa na ganin kowane yaro a jihar ya samu ingantaccen ilimi.
A yayin bikin rabon kujerun da ya gudana a ranar Juma’a, Gwamna Abba, ya jaddada muhimmancin samar da kayan karatu da za su taimaka wa ɗalibai wajen samun ilimi mai inganci.
Gwamnan, ya ce an ƙera kujerun cikin aminci kuma suna da ƙwari, wanda a cewarsa za su taimaka wa ɗaliban da ke ɗaukar karatu a yanzu da ma waɗanda za su zo daga baya.
Gwamnan, ya kuma gode wa matasa sama da 11,000, masu sana’ar kafinta da walda, waɗanda suka taka rawa gani wajen kammaluwar aikin.
ya jaddada cewar gwamnatinsa za ta ci gaba da taimakon matasa ta hanyar wajen bunƙasa sana’o’insu da kuma samar musu da aikin yi domin yaƙi da zaman banza.
Cikin wasu hotuna da Hadimin Kwankwasiyya Kan Kafofin Sadarwa, Ibrahim Adam, ya wallafa, an ga yadda gwamnan ya duba sabbin kujerun da aka ƙera.
Idan ba a manta ba, Gwamna Abba, ya sanya ilimi a sahun gaba cikin alƙawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaben 2023.
Ya ce ilimi shi ne zai zama sahun gaba a cikin abubuwan da zai fi mayar da hankali.
Ga hotunan kujerun da ya raba: