Kano: Abba ya sa hannu kan dokar karin masarautu uku

Sarakunan Masautun Gaya da Karaye da Rano za su kasance a karkashin jagorancin Sarkin Kano karkashin

Kano: Abba ya sa hannu kan dokar karin masarautu uku

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu kan dokar masarautu uku masu daraja ta biyu a a jihar.

A yammacin ranar Talata gwamnan ya sa hannu kan dokar, sa’o’i kadan bayan majalisar dokokin jihar ta amince da dokar masarautun.

Gwamnan ya sanya hannu ne kwanaki 51 bayan gwamantinsa ta rushe masarautu biyar masu daraja ta daya da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro a jihar.

Masarautun masu daraja ta daya da aka rushe su ne na Bichi, Gaya, Kano, Karaye da Rano, aka dawo da tsohuwar masarautar Kano, wadda a yanzu Sarki Muhammadu Sanusi II yake jagoranta.

Dokar da majalisar ta amince da ita a safiyar Talata ta nada sarakuna masu daraja ta biyu a sabbin masarautun Gaya, Karaye da kuma Rano.

Dokar ta sanya kananan hukumomi takwas a karkashin sabbin masarautun.

Masarautar Rano ta ƙunshi kananan hukumomin Rano, Bunkure da Kibiya.

Masarautar Gaya ta ƙunshi kananan hukumomin Gaya, Albasu da  Ajingi.

Ita kuma Masarautar Karaye ta ƙunshi kananan hukumomin Karaye da Rogo.

Duk sarakunan masarautun za su kasance a karkashin Sarkin Kano kuma za su kasance a matsayin abokan shawararsa.

 

Amincewa da dokar wadda ke jiran sa hannun Gwamna Abba Kabir Yusuf, na zuwa ne washegarin da Babbar Kotun Jihar Kano ta umarci tsoffin sarakunan , sarautu biyar na gwamnatin Ganduje daga gabatar da kansu a matsayin sarakunan jihar.

Kotun ta kuma umarci sarakunan rusassun asarautun na Bichi da Gaya da Kanon da Karar da kuma Rano da su dawonda duk kayan gwamnati da ke hannunsu.

NCC ta amince wa kamfanonin sadarwa ƙara kuɗin kira da data

Amurka jinsin mace da namiji kaɗai ta sani a hukumance — Trump

An rantsar da Donald Trump a matsayin Shugaban Amurka na 47

Za mu yi gwanjon motoci 891 da muka ƙwace — EFCC