Gwamnan Kano ya samu lambar yabo kan inganta ilimi

Gwamnan ya jadadda aniyarsa na ci gaba da inganta ilimi a jihar.

Gwamnan Kano ya samu lambar yabo kan inganta ilimi

Ƙungiyar Malaman Najeriya (NUT), ta bai wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf lambar yabo saboda gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen gyaran harkar ilimi a jihar.

Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya fitar ta bayyana cewa an ba da lambar yabon ne a bikin Ranar Malamai ta Duniya ta 2024 da aka yi a filin Eagle Square da ke Abuja.

Dawakin-Tofa, ya bayyana cewa an shirya bikin ne tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, inda aka tara malamai daga jihohi 36 na Najeriya don girmama waɗanda suka bayar da muhimmiyar gudunmawa a fannin ilimi.

An karrama Gwamna Yusuf ne saboda ƙoƙarin da ya yi na ceto tsarin ilimi a Jihar Kano daga durƙushewa.

Shugaban NUT na ƙasa, Kwamared Titus Ambe, ya bayyana cewa gwamnoni guda shida ne aka zaɓa karrama su, bisa jajircewarsu wajen inganta harkar ilimi, musamman ta hanyar tallafawa jin daɗin malamai da horar da su.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, daga cikin nasarorin da Gwamna Yusuf ya cimma har da ware kaso 29.9 na kasafin kuɗin Kano na shekarar 2024 ga ilimi.

Har wa yau, ya ayyana dokar ta-ɓaci a fannin ilimi, wanda hakan ya sa aka fara gyaran ginin makarantu da kuma samun ilimi mai inganci.

Da yake magana a madadin gwamnoni shida da aka karrama daga jihohin Borno, Oyo, Benuwe, Enugu, da Kebbi, Gwamna Yusuf ya tabbatar da cewa zai ci gaba da inganta harkar ilimi.

Ya jaddada muhimmancin inganta harkar don ganin cewa matasa sun samu ci gaba.

Da jami’an gwamnati nake zuwa tattaunawa da ’yan bindiga – Gumi

Gwamnan Kano ya samu lambar yabo kan inganta ilimi

Dalilin da ba a fara biyan masu hidimar ƙasa N77,000 ba — NYSC

2027: Neman tazarce ba ya gabana yanzu — Tinubu