Gwamnan Kano ya tura wa Majalisa sunayen kwamishinoni 19

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya tura wa Majalisar Dokoki sunayen mutane 19 da ya ke son naɗa wa a matsayin kwamishinoni. Shugaban Majalisar Dokokin Yusuf Falgore ne ya sanar da haka da safiyar Talata a zauren Majalisar. Honorabul Yusuf Falgore yace za a fara tantance kwamishinonin da ƙarfe 10:00 na safiyar Laraba. Shari’ar zaɓen […]

Gwamnan Kano ya tura wa Majalisa sunayen kwamishinoni 19

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya tura wa Majalisar Dokoki sunayen mutane 19 da ya ke son naɗa wa a matsayin kwamishinoni.

Shugaban Majalisar Dokokin Yusuf Falgore ne ya sanar da haka da safiyar Talata a zauren Majalisar.

Honorabul Yusuf Falgore yace za a fara tantance kwamishinonin da ƙarfe 10:00 na safiyar Laraba.

Shari’ar zaɓen Kano: Kotu za ta fara sauraron shaidu ranar Juma’a

Za a tada ganuwar Kano da ɓuraguzan rusau

Waɗanda za a tantance sun haɗa da mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam, shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano Honorabul Umar Haruna Doguwa, da tsohon kwamishinan lafiya a zamanin mulkin Injiniya Kwankwaso, Honorabul Abubakar Labaran Yusuf.

Sauran sun haɗa da tsohon shugaban ƙaramar hukumar Gwale, Honorabul Abbas Sani Abbas, shugaban ƙungiyar ɗaliban da gwamnatin Kwankwaso ta ɗauki nauyin karatunsu, Dr Yusuf Kofar Mata, da tsohon daraktan yaɗa labarai a gwamnatin Kwankwaso, Honorabul Baba Halilu Ɗantiye.

Akwai kuma Honorabul Ali Haruna Makoɗa, Honorabul Ɗanjuma Mahmoud, Honorabul Musa Shanono, Hajiiya Aisha Saji, Hajiya Ladidi Garko, Dr Marwan Ahmad, Injiniya Muhammad Diggol, Honorabul Adamu Aliyu Kibiya, Honorabul Hamza Safiyanu, Honorabul Tajo Usman Zaura, Sheikh Tijjani Auwal, Honorabul Nasiru Sule Garo, da Honorabul Haruna Isah Dederi.