Gwamnan Kano ya yi nadin mukamai a ranar farko

Sanarwar ta ce an zabi mutanen ne bisa la’akari da gogewarsu da kuma sadaukar da kai.

Gwamnan Kano ya yi nadin mukamai a ranar farko

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf

Sabon Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya nada rukunin farko na masu rike da makamai a gwamnatinsa, a ranar da aka rantsar da shi.

Sanarwar da sakataren gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar kasa da awa 24 da rantsar da da aka rantsar da shi su ne.

  1. Hon. Shehu Wada Sagagi, Shugaban Ma’aikata
  2. Abdullahi Baffa Bichi, — Sakataren Gwamnati
  3. Farouq Kurawa — Babban Sakataren Gwamna
  4. Hon. Abdullahi Ibrahim Rogo, Chief Protocol
  5. Sanusi Bature Dawakin Tofa, Babban sakataren yada Labarai

Sanarwar ta ce an zabi mutanen ne bisa la’akari da gogewarsu da kuma sadaukar da kai.